1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

February 24, 2006

Rikicin Nijeriya shi ne ya fi daukar hankalin Jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvQ2
Rikici a Nijeriya
Rikici a NijeriyaHoto: AP

A wannan makon mai karewa dai jaridun na Jamus sun fi mayar da hankalinsu ne ga mawuyacin hali na tashe-tashen hankula da kashe-kashe na ba gaira da aka fuskanta a Nijeriya da zaben kasar Uganda sai kuma halin da ake ciki a Darfur ta kasar Sudan..Amma da farko zamu duba rahoton jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ne, wanda ta gabatar a karkashin take: “Wata tsofuwar kurar rikici ta sake dabaibaye yanayin Nijeriya.” Jaridar ta ce:

“Sabanin da ake yi akan zanen batancin nan ga musulmi ya sake ta da kurar rikicin da aka dade ana fama da shi a Nijeriya. Murtane masu tarin yawa suka yi asarar rayukansu sakamakon matakai na kone-konen gidajen coci da masallatai, a dukkan arewaci da kudancin kasar. To sai dai kuma a a wannan karon ba ainifin sabanin zanen batancin ne musabbabin rikicin ba. Domin kuwa rahotanni sun ce wai wata malamar makaranta ce ta hana wata yarinya karanta alkur’ani a aji. Amma fa wannan bayanin na mai yin nuni ne da hali na zaman dardar da aka dade ana fama da shi tsakanin musulmi da kiristoci a Nijeriya.”

Ita kuwa jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta ambaci wasu majiyoyi ne na kungiyar Red Cross dake cewar:

“Mutane masu tarin yawa suka yi asarar rayukansu sannan wasu daruruwa suka ji rauni a baya ga dubbai da suka tagayyara sakamakon rikicin addini da ya sake billa a kasar Nijeriya. Wannan dai ba shi ne karo na farko da aka fuskanci irin wannan rikici mai nasaba da addini a kasar da ta fi kowace yawan jama’a a nahiyar Afurka ba. An sha fama da ire-iren wannan baraka tare da asarar dubban rayuka.”

Ita ma jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta leka Nijeriya domin bitar rikicin kasar da ya ki ci ya ki cinyewa, musamman a yankin Nigerdelta, wanda kuma ta ce yana mummunan tasiri akan tattalin wannan makekiyar kasa ta yammacin Afurka. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

“A sakamakon rikicin baya-bayan nan dake addabar Nijeriya kasar ta samu koma bayan yawan mai da take fitarwa zuwa ketare da misalin kashi 15%. Rikicin na Nijeriya a yankin Nigerdelta ya dauki wani sabon salo na garkuwa da ‘yan kasashen waje. Wannan mummunan ci gaba ko shakka babu zai dada gurgunta tattalin arzikin wannan kasa.”

Janhuriyar Demokradiyyar Kongo ta samu sabon daftarin tsarin mulki sakamakon goyan bayan da jama’a suka nunar a kuri’ar raba gardamar da aka kada watan desamban da ya wuce. Jaridar DIE TAGESZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“A yanzun dai ya rage watanni hudu da rabi ne kacal ga gwamnatin hadin gambiza da aka nada a karkashin wata yarjejeniya ta zaman lafiyar da aka cimma tsakanin kusan illahirin kungiyoyin da ba sa ga maciji da juna a janhuriyar demokradiyyar Kongo. To sai dai kuma mutane na tababa a game da yiwuwar gudanar da zaben da aka shirya nan gaba a wannan shekarar saboda kawo yanzu ba a albarkaci sabbin dokokin zaben ba.”

A can kasar Uganda dai tuni aka kammala zaben demokradiyya na farko da aka gudanar tun bayan da shugaba Museveni ya dare kan karagar mulki shekaru 20 da suka wuce. A lokacin da take sharhi game da haka jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

“Shugaba Yewori Museveni ya mika kai bori ya hau domin gudanar da wannan zabe da ya kunshi jam’iyyun siyasar barkatai ne sakamakon matsin lamba daga kasashen dake ba wa Uganda lamuni, wadanda ke daukar nauyin kashi 50% na kasafin kudin kasar dake kuryar tsakiyar Afurka. Take-takensa a yakin neman zabe kuwa ya taimaka murna ta koma ciki dangane da fatan da aka yi cewar za a kamanta adalci a zaben. Domin kuwa ko da yake binciken ra’ayin jama’a ya ba shi rinjaye, amma shugaban yayi bakin kokarinsa wajen gusar da babban abokin takararsa Kizza Besigye saboda fargabar rawar da dan hamayyar zai taka a zaben.”