Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 03.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Cutar murar tsuntsaye a Afurka ita ce ta dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus

Cutar murar tsuntsaye dake dada yaduwa a kasashen Afurka ita ce ta fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai karewa. Bisa ga ra’ayin jaridar BERLINER ZEITUNG kurakurai na mahukunta da kuma rashin wayar da kan jama’a ka iya mayar da cutar wata mummunar annoba a wannan nahiya. Jaridar sai ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

“A nahiyar Afurka mutane sun saba kiwon dabbobi a gidajensu. Mutane kan kiwata kaji da agwagi don amfanin kai da kai. To sai dai kuma kiwon ba yana tafiya ne akan wani nagartaccen tsari ba. Muddin cutar ta H5N1 ta rutsa da mutane ta kan dabbobin da suke kiwatawa to kuwa lamarin ka iya haddasa asarar rayukan dubban jama’a. Kawo yanzun dai ba wani rahoton dake nuna kamuwar dan-Adam da kwayar cutar a Afurka, amma matsaloli na rashin nagartacciyar hanyar kiwon lafiya da karancin abinci mai gina jiki ka iya kawo canji ga lamarin.”

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG mamaki tayi a game da rahoton dake cewar wai a wasu yankuna a Nijeriya mutane sun shiga sace kajin da suka kamu da kwayoyin cutar ta murar tsuntsaye. Jaridar sai ta kara da cewar:

“Bayanai daga wani mai aikewa da kamfanin dillancin labarai na AFP rahotanni sun yi nuni da cewar kimanin mutane talatin ne suka kutsa wani gidan gona suna masu wawason kajin da aka tanadar domin yankesu sakamakon kamuwa da cutar murar tsuntsaye. Bisa ga ra’ayin wadannan mutane dai matakin da aka dauka na yanke kaji kimanin dubu bakwai a wannan gidan gona ba kome ba ne illa barna kawai. Nijeriya dai ita ce ta farko da aka gano billar murar tsuntsayen a cikinta a nahiyar Afurka.”

Ita kuwa jaridar FRAKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG lekawa tayi kasar Uganda, inda ake sabani akan sakamakon zaben kasar da aka gudanar makon da ya wuce, wanda kuma ya ba wa shugaba Museveni gagarumin rinjaye. Jaridar ta ce:

“Ko da yake ‘yan hamayya na zargin magudi a zaben kasar Uganda da aka gudanar a makon jiya, amma wakilan sa ido daga kasashen Kungiyar Tarayyar Turai sun ce zaben ya tafi salin alin-ba tare da wata tangarda ba, kuma duka-duka kura-kuran da aka samu sun danganci matsaloli ne na fasahar gudanarwa. Amma duk da haka wakilan kungiyar sun gabatar da kira ga gwamnatin Museveni da ta canza salon kamun ludayinta ta yadda tsarin mulki na demokradiyya zai samu cikakkiyar karbuwa tsakanin al’umar kasar.”

Ita ma jaridar NEUES DEUTSCHLAND ta ba da rahoto akan daya zaben na kananan hukumomi a Afurka ta Kudu a wannan makon, inda take cewar:

“Shekaru 12 bayan kawo karshen mulkin wariya a Afurka ta Kudu, har yau bakar fata na ci gaba da fama da kaka-nika-yi a game da harkokin rayuwarsu ta yau da kullum a wannan kasa, inda aka wayi gari hatta gaggan jami’an jam’iyyar ANC dake mulki sai tare da cikakkiyar kariya ta jami’an tsaro ne suke iya kai da komo a unguwannin bakar fata. To sai dai kuma duk da haka, duk wanda yayi tsammanin samun canji a zaben kananan hukumomin da aka gudanar karo na uku tun bayan kawo karshen mulkin wariya a ATK tilas ne murnarsa ta koma ciki. Domin kuwa har yau ANC ce ke da fada a ji a harkokin yau da kullum a wannan kasa.”