1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

March 10, 2006

Jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne akan halin da ake ciki a Darfur

https://p.dw.com/p/BvQ0

Muhimman batutuwan da masharhanta na jaridun Jamus suka mayar da hankali kansu dangane da al’amuran Afurka a wannan makon sun hada da halin da ake ciki a Darfur da kuma kokarin da MDD ke yi na ganin an mayar da rundunar kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar afurka karkashin tutarta. A lokacin da take gabatar da rahoto akan haka jaridar FRNKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

“Har yau ana ci gaba da fama da sabani a game da tura sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD zuwa lardin Darfur domin su rufa wa rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afurka da aka tsugunar a lardin na yammacin Sudan baya. Bayan ganawar da suka yi da shugaba Kibaki na kasar Kenya a tsakiyar wannan makon, ministan harkokin wajen Sudan Muhammed Al-Wasila ya fito fili ya bayyana cewar kungiyar tarayyar Afurka ba ta da ikon mayar da sojojinta na kiyaye zaman lafiya a Sudan karkashin tutar MDD sai tare da amincewar gwamnati a fadar mulki ta Khartoum. A yau juma’a ne dai kungiyar zata tsayar da shawara game da haka a zauren taronta a Addis Ababa.”

A can kasar Kongo ma har yau ana fama da sabani a game da yiwuwar tura sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Turai domin sa ido akan zaben kasar da aka shirya gudanarwa nan gaba a wannan shekara. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

“Har yanzun dai ba a tsayar da shawara ba a game da ko shin KTT zata tura sojojinta zuwa kasar Kongo. Kungiyar dai tana cikin wani hali ne na tsaka mai wuya saboda sojoji masu tarin yawa da ta tura aikin kiyaye zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya. Amma duk da haka kungiyar ba ta so a ce ta gaza a fafutukar da take yi na samun fada a ji a siyasar duniya. Amma fa duk wata daula ta duniya wajibi ne ta san cewar ba abin kunya ba ne in ta ki ta kutsa kanta cikin gagari.”

Yau kimanin shekara daya ke nan da shugaban kasar Togo Gnassingbe Eyadema ya bakunci lahira, akan haka jaridar NEUES DEUTSCHLAND ta yi amfani da wannan dama domin ta duba halin da kasar ke ciki a yanzun. Jaridar dai karawa tayi ta cewar:

“Tun bayan mutuwar dan kama karya Gnassingbe Eyadema kawo yanzu babu wani canjin da aka samu dangane da take hakkin dan-Adam da ake yi a kasar Togo. Sojoji da dakarun sa kai kan kutsa gidajen mutane suna kame-kame da azabtar da fursinoni da fyade da dai sauran matakai na keta da rashin imani a karkashin magajin dan kama-karyar Faure Eyadema.”

Ita kuwa jaridar DIE WELT lekawa tayi kasar Zimbabwe, inda ta ce a yanzu shugaba Robert Mugabe na da ikon cin karensa babu babbaka sakamakon rarrabuwar hankulan da ake samu tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar hamayya ta MDC. Musabbabin wannan sabani kuwa shi ne zaben majalisar dattawan da aka gudanar watan oktoban bara, inda Tsivagirai yayi kiran kaurace wa zaben saboda a ganinsa gwamnati zata yi amfani da zaben ne domin ikirarin bin tafarkin demokradiyya. Amma bangaren masu goyan bayan zaben majalisar dattawan, abin da ya hada har da mataimakin shugaba Gibson Sibana da sakatare.janar na jam’iyyar Welshman Ncube sun ki amincewa da haka, saboda a ganinsu babban kuskure ne, abin da ya kaisu da zargin Tsivangirai da neman kasancewa wuka da nama a al’amuran jam’iyyar ta MDC.

Masu sauraro da wannan muke kammala rahotannin jaridun na Jamus akan al’amuran nahiyarmu ta Afurka. Zainab gare-ki.