1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

March 24, 2006

Kasar Kongo ita ce tafi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/BvPy
Thomas Lubanga
Thomas LubangaHoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

A wannan makon mai karewa dai ko da yake jaridu da mujallun Jamus sun fi mayar da hankalinsu ne akan kasar Kongo dangane da shawarar Kungiyar Tarayyar Turai na tura rundunar kwantar da tarzoma domin sa ido a zaben kasar da za a gudanar nan gaba a wannan shekara, amma duk da haka sun leka sauran sassa na Afurka domin tsegunta wa masu karatu irin wainar da ake toyawa a siyasar wannan nahiya. Misali jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta yi bitar kidayar jama’a a Nijeriya tana mai saka ayar tambaya a game da nasarar wannan mataki. Jaridar sai ta ce:

“Bai kamata ayi sako-sako da ire-iren abubuwan da zasu biyu bayan wannan manufa ta kidayar jama’a ba, wadda aka gabatar tare da nufin tantance ainifin yawan al’umar Nijeriya, kasar da ta fi kowace yawan jama’as a nahiyar afurka. Domin kuwa a karkashin daftarin tsarin mulkin kasar wajibi ne a raba madafun iko daidai da yawan kabilun da kasar ta kunsa. Kawo yanzun dai an dauka cewar Hausawa su ne suka fi yawa inda suka ninka Yarbawa da Ibo in an hade su waje guda. Idan har sakamakon kididdigar ya nuna akasin hakan to kuwa lamarin zai yi tasiri ga siyasar kasar ta Nijeriya.”

Ita kuwa jaridar DIE ZEIT mai fita mako-mako da yi nazari ne akan irin kyakkyawan ci gaban da ake samu a Nijeriya inda wasu shuagabannin addini ke bakin kokarinsu wajen ganin an yi kyakkyawan zama na cude-ni-in-cude-ka tsakanin mabiya addinai daban-daban a wannan makekiyar kasa wadda ta sha fama da rikice-rikicen addini. Jaridar ta ce a takaice ana iya lura da halin da duniya ke ciki na sabanin al’adu idan aka yi bitar kasar ta Nijeriya.

A wannan makon a karon farko aka gurfanar da daya daga cikin mutanen da ake tuhumarsu da ta’asar zub da jini a kasar Kongo gaban kotun kasa da kasa dake The Hague. Jaridar Berliner Zeitung ta yi sharhi akan haka tana mai cewar:

“Ire-iren wadannan mutanen suna da yawa a kasar Kongo, wasu daga cikinsu ma ana damawa da su yanzu haka a gwamnati. Amma duk da haka shari’ar da aka gabatar akan madugun ‘yan tawaye mai laifuka na ta’asar yaki Thomas Lubanga wata kyakkyawar alama ce dake ba da kwarin guiwa wadda kuma ta zo daidai lokacin da ya dace, ba ma kawai dangane da zaben kasar Kongo da za a gudanar nan gaba a wannan shekara ba. Lubanga shi ne na farko da aka gurfanar a gaban sabuwar kotun amsa miyagun laifuka ta kasa da kasa kuma shari’ar tasa zata zama darasi ga ire-iren madugannin kungiyoyin ‘yan ta kife masu cin karensu babu ba babbaka a wuraren da ake fama da rikici a duniya.”

Ita kuwa jaridar FRANKFUTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta yaba ne da irin rawar da Kungiyar Tarayyar Afurka ta taka a matakanta na kiyaye zaman lafiya a lardin Darfur. Jaridar sai ta kara da cewar:

“Abu daya mai nagartaccen tasiri dangane da rikicin lardin Darfur shi ne rawar da Kungiyar Tarayyar Afurka take takawa duk da rashin nasarar ayyukan sojojinta na kiyaye zaman lafiya su kimanin dubu bakwai da dari takwas da ta tsugunar a wannan yanki. Domin kuwa duk da rashin nasarar ayyukan sojojin wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma akalla kungiyar tayi namijin kokari wajen cika alkawarinta, ba maganar fatar baki kawai ba. Kuma gwamnatin Sudan ita ce ainifin ummal’aba’isin rashin nasarar matakin saboda kin ba da hadin kai da tayi. Amma duk da haka wannan mataki yana iya kasancewa na farko akan hanyar daga matsayin wannan kungiya ta hadin kan kasashen Afurka domin taka muhimmiyar rawa a siyasar duniya nan gaba.”