Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 31.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Cafke Charles Taylor da aka yi shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan mako

Charles Taylor a hannun mahukunta

Charles Taylor a hannun mahukunta

A wannan makon mai karewa dai babban abin daya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus shi ne cafke tsofon shugaban kasar Liberia Charles Taylor da aka yi da kuma danka shi a hannun MDD domin fuskantar shari’ar ta’asar miyagun laifuka na yaki a Saliyo da kuma ita kanta kasar Liberiya. Amma da farko zamu fara ne da duba ziyarar da shugaban kasar Jamus Horst Köhler zai kai ga wasu kasashe uku na nahiyar Afurka tun daga ranar lahadi mai zuwa. A lokacin da take gabatar da rahoto akan haka jaridar RHEINISCHE POST cewa tayi:

“Ana iya lura da yadda shugaban kasar Jamus Horst Köhler ya damu da makomar nahiyar Afurka ta la’akari da lafazin day a fito daga bakinsa lokacin da ake masa mubaya’a, inda yake cewar:”A zuciya ta makomar nahiyar Afurka it ace mizanin mutunta dan-Adam a wannan duniya tamu.” Wannan shi ne ya sanya shugaban yayi kiran shigar da sojojin Jamus a matakan kiyaye zaman lafiya dangane da zaben kasar Kongo da za a gudanar nan gaba a wannan shekara.”

A wannan makon ne aka tasa keyar tsofon dan kama karyar kasar Liberiya Charles Taylor zuwa Saliyo, inda aka danka shi hannun mahukunta na kotun kasa-da-kasa dake shari’ar ta’asar yakin basasar Saliyo domin fuskantar shari’a akan laifin da ake zarginsa da shi na sa hannu dumu-dumu a danyyen aiki da rashin imanin da aka aikata lokacin yakin. A cikin nata rahoton dangane da cafke Charles Taylor da aka yi bayan yunkurin rantawa a na-kare da yayi, jaridar SÜDDETUSCHE ZEITUNG cewa tayi:

“Cafke Milosevic din Afurka da aka yi domin gurfanar da shi gaban shari’a wani babban ci gaba ne domin karya alkadarin masu kokarin yin koyi da shi a yammacin Afurka. Charles Taylor dai shi ne shugaban wata kasa ta Afurka na farko da aka daukaka kara kansa a shekara ta 2003 akan laifuka na ta’asar yaki da cin mutuncin dan-Adam. Tsofon dan-kama-karyar ya dauki matakai iri-iri na rashin imani domin bannatar da kasashen Liberiya da Saliyo. Ana zargin Taylor da laifin iza keyar dakarunsa wajen kisan ba gaira ba dalili da azabtar da farar fula da dates gabobinsu, abin day a hada har da jarirai. A saboda haka ake masa taken “Milosevic din Afurka ta yamma.”

Ita kuwa jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU a ganinta cafke Taylor da aka yi ka iya zama gargadi ga ragowar tsaffin ‘yan kama karya da a halin yanzu suke more rayuwarsu a wuraren da suke zaman hijira, domin su shiga taitayinsu. Jaridar t ace wannan maganar ta shafi tsaffin ‘yan kama karya irinsu Hissene Habre na kasar Chadi dake zaman hijira a Senegal da Mengistu Haile Mariam na Habasha, wanda Robert Mugabe ya ba shi mafaka a Zimbabwe, ko da yake shi kansa Mugabe yana fargabar cewar ka da fa watan-wata-rana a wayi gari an gurfanar da shi gaban kotun kasa da kasa sakamakon matakansa na danne hakkin dan-Adam.