Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 14.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a Chadi na daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhantan Jaridun Jamus

Idriss Deby

Idriss Deby

A wannan makon jaridun Jamus sun mayar da hankalinsu ne akan sabon halin da aka shiga a kasar Chadi inda gwamnati ke fama da gwagwarmaya da ‘yan tawaye dake fafutukar kutsawa fadar mulki ta Njamena a kokarin kawar da shugaba Idriss Deby daga karagar mulki. A lokacin da take ba da rahoto game da wannan mawuyacin hali jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“An yi wata da watanni dakarun gwamnati da na ‘yan tawayen kungiyar neman kawo canji FUC suna gwabza fada a yankin gabacin kasar Chadi a iyaka tsakaninta da kasar Sudan. Amma a yanzun tuni fadan ya zarce zuwa yankin Mongo kuma ‘yan tawayen na kokarin kutsa kai Njamena. A sakamakon haka ne gwamnatin Faransa ta sanya sojojinta dake Chadi a cikin shirin ko-ta-kwana sannan ta ce zata tura karin dakarun soja 150 zuwa Chadin. Ga alamu dai wannan rikici yana da nasaba da cinikin mai da kasar Chadi ta fara fitarwa zuwa ketare tun a shekara ta 2003. Rabon wannan arziki na man fetur ita ce ta kawo rarrabuwa tsakanin magabatan wannan kasa. Shi kansa tsofon ministan mai na Chadi Tom Erdimi yana zaman hijira a Texas ta Amurka yanzu haka, yana kuma ikirarin cewar shi ne madugun ‘yan tawayen. Amma a daya bangaren su kansu ‘yan tawayen kawunansu ya rarrabu, inda wasu daga cikinsu ke samun goyan baya daga gwamnatin Sudan, wadansunsu kuma na samun goyan baya daga ‘yan tawayen lardin Darfur.”

Ita kuwa jaridar LE MONDE DIPLOMATIQUE mai fita da harshen Jamusanci ta sake lekawa ne can yankin Nigerdeltan Nijeriya, inda take cewar a yayinda a bangare guda wasu ke cin ribarsu daga arzikin mai a daya bangaren kuma akwai masu cin riba ta hanyar ta da kayar baya. Jaridar sai ta kara da cewar:

“Wani abin lura da tarihin mulkin demokradiyyar Nijeriya dan shekaru bakwai shi ne kasancewar gwamnatin da aka nada tayi alkawarin yaki da matsalar cin hanci da ba da la’akari ga matakan kare kewayen dan-Adam domin kyautata jin dadin rayuwar mazauna yankunan kasar dake da dimbim albarkatun mai. Amma fa daga cikin ribar dalar Amurka miliyan dubu 350 da Nijeriya ta samu daga cinikin mai tun bayan samun ‘yancin kanta kawo yanzu an rasa makomar dala miliyan dubu 50. A saboda haka bai zama abin mamaki ba ganin yadda ake samun tawaye da ta da kayar baya a yankunan da ake hako man, saboda mazauna wadannan yankuna sune suka fi jin radadin matsalar cin hancin da bannatar da kewayen dan-Adam da gaggan kamfanonin ketare ke yi ba kakkautawa.”

Kimanin mutane dubu 700 suka yi asarar gidajensu a wani matakin da gwamnatin shugaba Robert Mugabe ta dauka da sunan tsaftace birnin Harare a shekarar da ta wuce. Jaridar DIE WELT ta sake bitar halin da wadannan tagayyararru suke ciki ta kuma gabatar da rahotonta dake cewar:

“Wadannan mutane da aka fatattaka daga gidajensu suna cikin mawuyacin hali na rayuwa, saboda zama suke hannu baka hannu kwarya suna masu dogara akan taimakon da suke samu daga ‘yan hamayya. A dai wannan marra da ake ciki yanzu duk abin da mutum ke bukata a kasar Zimbabwe, kama daga abinci zuwa magunguna da man fetur da taki sai dai ya saya a kasuwannin bayan gida. A cikin watanni 12 kacal farashin burodi ya ribanya da misalin kashi 2100 cikin dari.”