Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 21.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Tasirin arzikin man fetur a rikice-rikicen Afurka shi ne ya dauki hankalin jaridun Jamus

Rijiyar hakar mai a Chadi

Rijiyar hakar mai a Chadi

Mawuyacin halin da ake ciki a jihar Nigerdeltan Nijeriya na daga cikin batutuwan da masharhanta na Jaridun Jamus suka duba a wannan makon mai ƙarewa. A cikin nata rahoton jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“Duk dai wanda yayi batu a game da masu ta da ƙayar baya a yankin Nigerdelta yana nufin wata ƙungiya ce mai fafutukar farfado da al’amuran wannan yanki wadda ke kiran kanta MEND a taƙaice. Tun bayan ɓliiarta misalin shekara ɗaya da ta shige ƙungiyar MEND ke da alhakin rayukan sojoji da ‘yan sanda masu tarin yawa da suka salwanta. Kazalika tayi mummunar illa ga tattalin arzikin Nijeriya a watannin baya-bayan nan. Dakarunta sun riƙa kai hari kan kafofin haƙar mai tare da yin garkuwa da ma’aikata daga ƙasashen ƙetare, wadanda bisa ta bakin kakakinta Bello Oboko wai fursinonin yaƙi ne, ko da yake daga baya an sake su. Wannan rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa yana mummunan tasiri akan farashin mai a kasuwannin duniya.

Ita ma dai jaridar Berliner Zeitung ta yi matashiya ne da rikice-rikice na siyasa irin shigen wadanda ake fama da su a Nijeriya da Chadi da kuma kai ruwa ranar da ake yi da ƙasar Iran game da kasancewa ummal’aba’isin hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya. Jaridar sai ta ƙara da cewar:

“Wani abin lura a nan shi ne rikicin ƙasashen Afurka masu arziƙin mai kamar Nijeriya da Sudan da kuma Chadi yana daɗa yin tsamari ne sakamakon muhimmancin man a kasuwannin duniya. A baya ga ƙasar Amurka, ita ma ƙasar China na daga cikin gaggan masu cin gajiyar arzikin man da Allah Ya fuwace wa ƙasashen Afurka yanzu haka.”

Rikicin da ake fama da shi a ƙasar Chadi kuwa abu ne da zai iya ƙara tabarbara halin da ake ciki a yankin Darfur na ƙasar Sudan, in ji jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG, wadda ta kara da cewar:

“Dalilin haka kuwa shi ne kasancewar ‘yan tawayen ƙasar Chadi dake adawa da mulkin shugaba Idriss Deby sun mayar da lardin Darfur na yammacin Sudan wani dandali na shirya hare-harensu na sare ka noke. A saboda haka ya zama wajibi akan kafofi na ƙasa da ƙasa su yi bakin ƙoƙarinsu wajen hana ƙazancewar rikicin, in kuwa ba haka ba su kansu jami’an taimako zasu shiga ƙaƙa-nika-yi game da makomar ayyukansu.”

Ita kuwa jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU leƙawa tayi ƙasar Cote d’Ivoire, wadda ta ce nasarorin da ta samu a zamanin baya shi ne ainifin musabbabin rikicin da take fama da shi yanzun. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Kasar Cote d’Ivoire ta samu bunƙasar tattalin arziki a cikin shekaru 30 da suka biyo bayan ‘yancin kanta a ƙarƙashin marigayi Felix Houphouet Boingy. Bayan mutuwarsa a 1993 da kuma faduwar farashin koko da ƙasar ta dogara akansa wajen samun kuɗaɗen shiga al’amura suka rikiɗe suka ɗauki wani sabon fasali kuma nan da nan matsalar ƙabilanci ta kunno kai inda ‘yan kudancin ƙasar ke nuna cewar wai sune ‘yan Cote d’Ivoire tsantsan, sannan su kuma ‘yan arewacinta dake da dangantaka da ƙabilun ƙasashen Mali da Burkina Faso baƙi ne. Wannan rikici shi ne ya kai ga rarrabuwar ƙasar gida biyu, inda ‘yan tawaye ke riƙe da arewaci su kuma magoya bayan shugaba Laurent Gbagbo ke da ikon kudancinta. A dai halin yanzu an sake komawa zauren shawarwarin sulhu tsakanin sassan biyu tare da fatan cewar za a cimma daidaituwa domin sake mayar da ƙasar ƙarƙashin inuwarta ta zaman lafiya da kwanciyar hankali.”