Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 05.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a Darfur shi ne ya fi ɗaukar masharhanta na jaridun Jamus

China a Afurka

China a Afurka

A wannan makon halin da ake ciki dangane da shawarwarin sasanta rikicin Darfur ta ƙasar Sudan shi ne ya fi ɗaukar hankalin jaridun na Jamus. Amma da farko zamu fara ne da duba rahoton jaridar GENERAL-ANZEIGER ta birnin Bonn a game da abin da take gani tamkar gwagwarmayar ɗora hannu akan arzikin man Nijeriya. Jaridar dai cewa tayi:

“A ƙoƙarinsa na dakatar da tashin-tashinar da ake fama da ita a yankin Nigerdelta shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo yayi wa mazauna yankin alkawarin samar musu da sabbin guraben aiki da kuma wata sabuwar hanyar mota samfurin ƙare gudunka. Fatansa dai shi ne wannan alkawarin zai taimaka al’umar yankin su daina rufa wa ‘yan tawaye baya, waɗanda a watannin baya-bayan nan suka gurgunta ayyukan haƙar kashi ɗaya bisa biyar na man a Nijeriya wanda ya taimaka wajen tashin gwauron zabon da farashinsa yayi a kasuwannin duniya.”

Ita kuwa jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta mayar da hankalinta ne ga fafutukar da China ke yi domin tabbatar da angizonta a nahiyar Afurka, inda take cewar:

“A yayinda ƙasashen yammaci, abin da ya haɗa har da Jamus suka fi mayar da hankalinsu ga matsaloli na yunwa da yaƙe-yaƙe na basasa dake addabar nahiyar Afurka, ita China a ɗaya ɓangaren tana ƙoƙari ne ta ɗaga martabar wannan nahiya a matsayin babbar abokiyar burmin cinikinta, inda zata riƙa shigar da kayayyakinta zuwa ƙasashen na Afurka tare da cin gajiyar arzikin mai da sauran albarkatun ƙasa da Allah Ya fuwace wa nahiyar. Wannan shi ne ainifin manufar ziyarar da shugaba Hu Jintao ya kai ga wasu ƙasashe na Afurka a makon da ya gabata, inda a Nijeriya aka cimma yarjejeniya akan wasu sabbin rijiyoyin mai guda huɗu da za a danƙa wa China alhakin tafiyar da al’amuransu, biyu a yankin rikici na Nigerdelta sannan biyu kuma a tafkin Chadi.”

Akwai alamun sake ƙazancewar yaƙin Darfur dake yammacin Sudan in ji jaridar DIE TAGESZEITUNG tana mai ɗora laifin hakan akan kafofi na ƙasa da ƙasa dake sako-sako da wannan rikici. Jaridar ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

“A yayinda ake fama da tafiyar hawainiya a shawarwarin zaman lafiyar Darfur a Abujan Nijeriya, a ɗaya hannun kuma ana ci gaba da fafata yaƙi a lardin na yammacin Sudan ba ƙaƙƙautawa. Kimanin mutane dubu metan aka fatattaka daga gidajensu tun abin da ya kama daga farkon wannan shekara. Ya zama tilas ƙungiyoyin ba da taimako su janye jami’ansu daga wasu yankuna da dama sakamakon mawuyacin halin da ake fama da shi. A makon da ya gabata, kamar yadda rahotanni masu nasaba da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan-Adam suka nunar, sojojin gwamnati sun gabatar da matakai na farmaki tare da samun rufa baya daga jiragen saman yaƙi a yankunan dake kewayen Gereida da Joghana, inda ‘yan tawaye ke da angizo. A sakamakon haka wakilin MƊD Jan Egeland ke gargaɗi a game da taɓarɓarewar matakan taimakon ma baki ɗaya.”