1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

May 19, 2006

Jaridun Jamus sun ba da la'akari da ci gaban da ake samu a siyasar Nijeriya

https://p.dw.com/p/BvPs
Taswirara Nijeriya
Taswirara NijeriyaHoto: AP Graphics

Ko da yake shawarar da majalisar ministocin Jamus ta tsayar a game da shigar da sojojin kasar a rundunar kiyaye zaman lafiya ta Kungiyar Tarayyar Turai da za a tura kasar Kongo ita ce ta fi daukar hankalin masharhanta a game da al’amuran Afurka, amma duk da haka ba su yi watsi da abubuwan dake faruwa a sauran sassa na nahiyar ba, musamman ma Nijeriya dangane da jana’izar shirin ta zarce da majalisar dattawa da ta wakilan Nijeriya suka yi a wannan makon. A cikin sharhin da ta bayar a karkashin taken: “Ba za a yi wa Nijeriya wani shugaba na rai-da-rai ba” jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“Ba zato ba tsammani a ranar talatar da ta wuce wakilan majalisar dattawan Nijeriya suka shiga runguma da yi wa juna barka sakamakon shawarar da suka yanke na yi fatali da maganar garambawul ga daftarin tsarin mulkin kasar da zai ba wa shugaba Olusegun Obasanjo damar sake tsayawa takarar zabe shekara mai zuwa domin wa’adin mulki karo na uku. Wannan kuwa, kamar yadda daya daga cikin wakilan majalisar dattawan ya nunar wata babbar nasara ce ga tsarin mulkin demokradiyya.” Domin kuwa wani binciken ra’ayin jama’a da aka gudanar ya nuna cewar sama da kashi 70% na al’umar Nijeriya ke adawa da manufar da aka saninta da ta zarce.”

Bisa ga dukkan alamu rikicin kasar Somaliya ya dauki wani sabon fasali, inda ya kauce daga yaki na kabilanci zuwa yaki na addini, in ji jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU lokacin da take ambaton ta bakin darektan kungiyar neman zaman lafiyar Somaliya Shirwa Abdullahi. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

“Tun misalin mako daya da ya wuce ake fafatawa tsakanin bwata kungiya mai kiran kanta wai kungiyar yaki da ta’addanci dake samun daurin gindin Amurka da dakarun sa kai na Musulmi. Ita dai Amurka dalilin da ta bayar a game da rufa wa kungiyar da take yi shi ne wai saboda ka da ta’addanci ya samu wata kafa ta yaduwa a yankin gabacin Afurka. Amma fa a daya hannun dakarun sa kai na wata kungiya ta musulmi mai tsananin kishin addini sai dada farin jini suke samu tsakanin jama’a, inda ake yaba musu da sake maido da doka da oda a birnin Mogadishu, wanda kashi 80% na fadinsa ke karkashin ikonsu.”

A wannan makon ne majalisar ministocin Jamus ta amince da manufar shigar da sojojin kasar a rundunar kiyaye zaman lafiya da Kungiyar Tarayyar Turai zata tura zuwa kasar Kongo domin sa ido akan zaben kasar da aka shirya gudanarwa a karshen watan yuli mai zuwa. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta gabatar da rahoto tana mai cewar:

“Wani abin da ake tsoro a game da zaben na kasar Kongo shi ne wani fada da zai iya barkewa tsakanin magoya bayan shugaba Kabila da mayakan mataimakinsa kuma tsofon madugun ‘yan tawaye Jean-Pierre Bemba dangane da sakamakon zaben. Akwai dai jita-jitar cewar Bemba ya dirke dakarunsa kimanin dubu biyar a kusa da Kinshasa, wadanda ke cikin shirin ko-ta-kwana. A daya bangaren kuma shugaba Kabila na da dubban-dubatar mayaka, wadanda dukkansu suka fito daga lardin Katanga kuma ba sa shayin amfani da karfin bindiga in har sakamakon zaben bai zo musu da dadi ba. Wannan ma shi ne ya sa Kabila ya rika kyamar shawarar tura sojojin na kasashen Turai, saboda a ganinsa mataki ne na nuna adawa gare shi. Akalla dai su kansu al’umar kasar na madalla da wannan mataki saboda zai tabbatar musu da tsaro, kuma wannan ba shi ne karo na farko da sojojin na Turai suka tara rawar gani wajen shiga tsakani domin dakatar da tashe-tashen hankula a nahiyar Afurka ba.”