Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 07.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Shugaba Museveni zai yi afuwa ga 'yan tawaye in an samu ci gaba a shawarwarin zaman lafiya

Bakin haure daga Senegal

Bakin haure daga Senegal

Sabon hali da aka shiga a kasar Uganda, inda gwamnati ta bayyana shirinta na afuwa ga dakarun kungiyar tawaye ta LRA domin cimma zaman lafiyar kasar na daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon, inda misali jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG take cewar:

“Ba zata ba tsammani shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya ba da sanarwa akan shirinsa na yi wa madugun kungiyar tawayen LRA a arewacin Uganda, Joseph Kony, afuwa idan har an cimma nasara a shawarwarin zaman lafiya tare da kungiyar. Shugaban na Uganda yayi kakkausan suka akan MDD, wadda ya ce ta gaza wajen cafke Kony da kuma gurfanar da shi gaban kotun kasa da kasa don amsa laifukan ta’asar yaki da ake zarginsa da shi. Ita dai kungiyar LRA ita ce ke da alhakin hijirar mutane sama da miliyan daya daga arewacin Uganda, inda ake zarginta da laifukan da suka hada da gurgunta gabobin mutane da yi wa mata fyade da kusan kare dangi da kuma sace farar hula domin yin garkuwa da su.”

A ganawar da suka yi lokacin taron kolin kasashen kungiyar hadin kan Afurka ta AU a Banjul fadar mulkin kasar Gambiya a karshen makon da ya wuce, ba a cimma daidaituwa ba tsakanin sakatare-janar na MDD Kofi Annan da shugaban kasar Sudan umar Al-Bashir dangane da kara wa’adin aikin sojan kiyaye zaman lafiya na MDD a lardin Darfur, kamar yadda jaridar FRANKFURTEr ALLGEMEINE ZEITUNG ta rawaito ta kuma kara da cewar:

“Duk da rashin cimma daidaituwa dukkan sassan biyu sun amince akan ci gaba da tuntubar juna. A sakamakon karancin kudi kungiyar hadin kan Afurka ta AU ta tsayar da shawarar janye dakarun sojanta su 7000 daga Darfur nan da karshen shekara.”

A sakamakon kasa cimma daidaituwa da aka yi akan yarjejeniyar kamun kifi tsakanin Senegal da kungiyar tarayyar Turai, kasar ta Senegal a wannan makon ta haramta wa jiragen ruwan kamun kifi na kasashen kungiyar zirga-zirga a gabar tekunta. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar DIE TAGESZEITUNG nuni tayi da cewar:

“Kasar Senegal ta dogara ne akan ayyukan kamun kifi domin samun kashi daya bisa uku na kudaden shigarta kuma a ‘yan watannin baya-bayan nan masuntan kasar sun sha bayyana adawarsu da sabunta yarjejeniyar kamun kifin da Kungiyar Tarayyar Turai domin kuwa masunta daga kasashen kungiyar na amfani ne da manyan jiragen ruwan kamun kifi dake gurkunta ayyukan kananan masunta na kasar Senegal. Bugu da kari kuma wannan kwarar da ake wa masuntan Senegal, inda su kan tashi a tutar babu, na daya daga cikin abubuwan dake tasa keyar bakin haure domin yin kaura zuwa nahiyar Turai.”

A kasar Muzambik dake kudancin Afurka gwamnati ta fara amfani da dakarun tsaro ‘yan sa kai domin tinkarar miyagun laifuka da matsaloli na tashe-tashen hankula tsakanin jama’a. A lokacin da take rawaito rahotonta game da wannan ci gaba jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU cewa tayi:

“Mutane na marhabin da wannan shawara da gwamnati ta gabatar tun misalin shekaru uku da suka wuce, saboda jami’an tsaron na sa kai sun san ire-iren matsalolin dake addabar talakawan kasa da kuma abubuwan dake ci musu tuwo a kwarya bisa sabanin mahukunta na ‘yan sanda, wadanda ba abin da yayi musu zafi game da wadannan matsaloli.”