1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

July 14, 2006

Halin da ake ciki a Somalia na daga cikin batutuwan Afurka da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPn
Dakarun kungiyar Islama a Mogadishu
Dakarun kungiyar Islama a MogadishuHoto: AP

Sabon halin da aka shiga a kasar Somaliya na daga cikin batutuwan da suka mamaye kanun labaran jaridun Jamus a wannan makon. A lokacin da take tabo wannan batu jaridar GENERAL ANZEIGER ‘yar Bonn cewa tayi:

“Mayar da birnin Mogadishu da kungiyar musulmi mai zazzafar akida tayi abu ne da tuni ya jefa gwamnatin rikon kwarya ta kasar Somaliya cikin mawuyacin hali game da makomar ikonta. Domin kuwa a yayinda ita gwamnatin wucin gadin tsaffin madugwannin yakin kasar ne ke da fada a ji, wadanda kuma tuni al’umar Somaliya suka kosa da al’amuransu, ita kungiyar ta musulmi dake da zazzafar akida sai dada samun karin magoya baya take yi, ganin cewar akalla a yankunan dake karkashin ikonta ana biyayya ga al’amuran doka da oda, duk kuwa da sabanin dake tsakanin ‘ya’yanta masu zazzafa da kuma masu matsakaicin ra’ayi na akidar addini.”

A daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaben kasar Kongo a ranar 30 ga wannan wata, gwamnati a fadar mulki ta Berlin tayi wa kasar alkawarin taimako bayan kawo karshen aikin kiyaye zaman lafiya na sojan kasashen Kungiyar Tarayyar Turai, kamar yadda jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta rawaito ta kuma kara da cewar:

“Ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung shi ne yayi wa sakatare-janar na MDD Kofi Annan wannan alkawari lokacin da suka gana a birnin Berlin a farkon wannan mako. Kazalika shi kansa ministan a lokacin da ya kai ziyara birnin Kinshasa sai da yayi wa kasar Kongo alkawarin ba da taimakon sake gina kasar a karkashin duk wata gwamnatin da za a nada sakamakon zaben demokradiyyar da za a gudanar karo na farko a kasar a ranar 30 ga watan yuli. Kasar na bukatar taimako wajen gyara al’amuranta na tsaro da ba da horo ga ‘yan sanda da kuma kyautata manufofin gwamnati a al’amuran gudanarwa, kuma Jamus a shirye take ta ba da taimako a wannan bangaren.”

Har yau dai ana fama da matsalar tuttudowar ‘yan gudun hijirar Afurka zuwa nahiyar Turai, wanda a wannan karo yawan nasu ya kai intaha, a cewar jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU. Jaridar ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

“A halin yanzu haka an kisayce cewar akwai akalla mutane sama da dubu tamanin dake kan hanyarsu ta yin kaura daga Afurka zuwa Turai. Kimanin dubu 50 daga cikinsu da su bi ta kan kasar Mauritaniya sannan wasu dubu 20 kuma su yi amfani da gabar tekun Senegal domin shigowa Turai. Nahiyar Turai ba zata iya shawo kan wannan matsala ba sai fa idan ta ba da kyakkyawan hadin kai, wanda zai gamsar da dukkan kasashen da lamarin ya shafa.”

A shekara ta 2010 kamar yadda aka shirya idan Allah Ya kai mu, za a gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Afurka ta Kudu, kuma tuni kasashen Afurka suka dokata suna tattare da fatan cewar wannan gasar zata ba wa kwallon kafa cikakkiyar nasara a wannan nahiya. To ko shin kazalika gasar zata taimaka wajen ta da komadar tattalin arzikin kasashen nahiyar? Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ce ta saka wannan ayar tambayar, sannan ta ci gaba da cewar:

“Lamarin ya danganta ne da alkiblar da za a fuskanta dangane da manufofin raya kasa da wadanda zasu zuba kudi domin tafiyar da gasar a Afurka ta Kudu da kuma abin da zai faru ga ribar da za a samu. Wasu dai na da ra’ayin cewar wajibi ne a samu kwarara makudan kudi zuwa nahiyar Afurka, a yayinda wasu kuma ke ba da fifiko ga matakan yaki da cin hanci da tabbatar da mulkin demokradiyya.”