1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

September 22, 2006

Tabargazar jibge dagwalon masana'antu mai guba a kasashen Afurka na daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPe

Halin da ake ciki a lardin Darfur na kasar Sudan na daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus akan al’amuran Afurka a wannan makon mai karewa, inda a cikin nata rahoton jaridar DIE TAGESZEITUNG take nuni da yadda ake dada samun kiraye-kiraye daga dukkan sassa na duniya a game da katsalandan soja a Darfur domin kawo karshen ta’asar kisan kiyashin dake ci gaba da wanzuwa a wannan yanki na yammacin kasar Sudan. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Wai shin sai bayan an kashe mutane miliyan daya ne MDD zata tura dakarunta domin katsalandan a lardin Darfur, daidai da yadda lamarin ya kasance a kasar Ruwanda a shekara ta 1994. Ita kanta kasar Ruwanda a halin yanzu haka tana da sojoji masu tarin yawa a tsakanin rundunar kiyaye zaman lafiya da kungiyar tarayyar Afurka ta tsugunar a Darfur kuma tuni ta mayar da yaki da ta’asar kisan kare-dangi, wani muhimmin abin da take ba wa fifiko a manufofinta na ketare.”

Ita kuwa jaridar DIE ZEIT mai fita mako-mako ta mayar da hankalinta ne akan tabargazar zubar da dagwalon masana’antu mai guba da sauran tarkacen da ba su da sauran alfanu ga wadannan kasashen a kasashe masu tasowa. Jaridar ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

“Mummunar ta bargaza ta farko da aka gano ta wakana ne a shekarar 1988 lokacin da aka jibge ganguna kimanin dubu biyu na shara mai guba daga kasar Italiya a tashar jirahen ruwan Koko a Tarayyar Nijeriya. Mutane sun kamu da cututtuka sakamakon wannan guba, ita kuma gwamnatin Nijeriya bata yi wata-wata ba wajen janye jakadanta daga birnin Rom da kuma tsare wani jirgin ruwan dako na Italiya domin tilasta kwashe sharar gubar daga harabar kasar. A kuma halin da ake ciki yanzu haka a na nan ana fama da kaka-nika-yi da wani dagwalon masana’antun mai guba da haddasa rashin lafiyar mutane sama da dubu 30 a Abidjan, cibiyar kasuwancin kasar Cote d’Ivoire. Amma fa wannan wani bangare ne na tabargazar. Domin kuwa tuni kasashe masu tasowa suka zama bolar zub da sharar tsaffin kayayyakin alatu, kamarsu rediyo da telebijin da komputa da dai sauran kayayyakin lantarki da basu da wata moriya ga kasashe masu ci gaban masana’antu.”

A yayinda a bangare guda ake ci gaba da tursasa wa ‘yan hamayya a kasar Zimbabwe, a daya bangaren kuma kasar na fama da mummunar hauhawar farashin kayan masarufi da misalin kashi 1200 cikin dari kamar yadda jaridar GENERAL-ANZEIGER ‘yar Bonn ta nunar. Jaridar ta ce:

“An samu tsadar farashin gidajen haya da abinci da sauran muhimman kayayyakin biyan butaku na yau da kullum da misalin ninki goma sha uku idan an kwatanta da shekarar da ta wuce ba tare da ma’aikata sun samu karin albashi ba. Su kuma ‘yan kodago da suka yi kurarin shiga zanga-zanga domin bayyana wa gwamnati irin mawuyacin halin da suke ciki mahukunta ba su yi wata-wata ba wajen murkushe su tare da lallasa sakatare-janar na kungiyar kodago Wellington Chibebe har sai da aka kwantar da shi a asibiti. Shugaba Mugabe na amfani da karfin hatsi ne domin danne duk wata kurar da ka taso ta nuna kin amincewa da salon kamun ludayinsa.”