1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

October 6, 2006

Rikicin Darfur shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPc
Darfur
DarfurHoto: AP

Halin da ake ciki a yankin Darfur na kasar Sudan, inda al’amura ke dada tabarbarewa tare da barazanar jefa yankin gabaci da tsakiyar Afurka cikin hali na zaman dardar da rashin sanin tabbas, shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon, inda jaridar DIE TAGESZEITUNG take cewar:

“A yayinda shugaban kwamitin zartaswa na kungiyar tarayyar Afurka Alpha Oumar Konare ke batu a game da wani sabon salo na yaki a lardin Darfur, takwaransa Jose Maria Barroso na kungiyar tarayyar Turai kwatanta lamarin yayi da ta’asar kasar Ruanda inda duniya gaba dayanta ta zura ido ba tare da an dauki wani takaimaiman mataki na tinkarar lamarin ba. Shi kuwa sakatare-janar na MDD Kofi Annan gargadi yayi a game da barazanar da ake fuskanta wajen jefa yankin tsakiyar Afurka cikin mawuyacin hali na zaman dardar.”

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG a cikin nata sharhin cewa tayi:

“Nahiyar Turai ba zata samu kwanciyar hankali ba face idan makobciyarta Afurka ta samu sararawar al’amuranta, a sakamakon haka kungiyar tarayyar Turai ke bakin kokarinta wajen mara wa kawarta kungiyar tarayyar Afurka baya domin shawo kan matsalolin dake addabar nahiyar ta Afurka, musamman ma mawuyacin halin da ake ciki a rikicin lardin Darfur da yaki ci ya ki cinyewa a yammacin kasar Sudan. Kungiyar Tarayyar Turai zata taimaka wa ta tarayyar Afurka da tsabar kudi Euro miliyan 55 domin cike gibin kasafin kudinta da ya kama Euro miliyan 70 a shekara.”

Ministocin tsaro na kasashen KTT sun hakikance cewar sojojin kiyaye zaman lafiya da kungiyar ta tura zuwa kasar Kongo zasu kammala aikinsu a daidai wa’adin da MDD ta kebe musu na ranar 30 ga watan nuwamba mai zuwa. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG karawa tayi da cewar:

“Ko da yake kantoman KTT akan manufofin ketare Javier Solana ya bayyana cewar bai ga wani dalilin da zai sanya a kara wa’adin aikin sojojin kiyaye zaman lafiyar na Eufor a kasar Kongo bayan zagayen zabe na biyu domin fid da gwani tsakanin shugaba mai ci Josef Kabila da abokin takararsa Jean-Pierre Bemba ba, amma kungiyoyi na kasa da kasa dake zaman kansu na bakin kokarinsu wajen ganin lalle sojojin sun ci gaba da aikinsu na tsaron zaman lafiya domin hana billar rikici bayan zaben na fid da gwani. A zagayen farko na zaben dai sai da dakarun sojan na Eufor suka kwantar da kurar wata tarzomar da ta biyo baya, lamarin da ya daga martabarsu a idanun al’umar Kongo, musamman ma mazauna Kinshasa, fadar mulkin kasar.”

A nata bangaren mujallar DER SPIEGEL mai fita mako-mako sharhi tayi akan tabargazar zub da dagwalon masana’antu mai guba da kasashe masu ci gaban masana’antu ke yi a nahiyar Afurka, inda take cewar:

“A sakamakon tabargazar baya-bayan nan dangane da dagwalon masana’antu mai guba da aka jibgie a Abidjan, cibiyar kasuwancin Cote d’Ivoire a yanzu ya zama wajibi gwamnatocin kasashen Turai su tashi haikan wajen binciken ire-iren abubuwan da jiragen ruwansu na jaura ke dauke dasu. Domin kuwa ita wannan tabargazar ta Probo Koala, ita ce aka gano, amma ba wanda ya san tahakikanin yawan dagwalon da ake zubarwa yanzu haka a nahiyar Afurka, wacce ke fuskantar barazanar zama bolar dattin masana’antu mai guba. Wani abin lura game da wannan tabargaza shi ne yadda mahukuntan tashar jiragen ruwan Estoniya suka ba wa jirgin ruwan Probo Koala damar dangana a wannan tasha duk da rahotannin tabargazar da ya yadu a dukkan kafofin yada labarai na duniya.”