1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

October 13, 2006

Halin da ake ciki a Niger Delta ya shiga kannun rahotannin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPb

Maganar garkuwa da fursinoni a yankin Nigerdeltan Nijeriya na daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotanni da sharhunan jaridun Jamus a wannan makon. A cikin nata rahoton jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

“Kafofin hakan man Nijeriya a yankin Nijerdelta sun sake shiga mawuyacin hali sakamakon garkuwar da ake ci gaba da yi da ma’aikatan kamfanonin mai a wannan yanki. Gaggan masana sun kiyasce cewar mai yiwuwa Nijeriya, wadda ita ce ta uku a cikin jerin kasashen dake cinikin mai a duniya, ta fuskanci gibin kashi 25% na yawan mai da take haka a wannan shekarar sakamakon wadannan rigingimu. Kamfanin Shell kadai ya ce ya kan samu gibin garewani dubu 480 dangane da yawan mai da yake hakowa a rana.”

A karo na farko kasar Spain tayi wa wata kasa ta Afurka alkawarin ba ta wani kaso na ‘yan kaka-gida da zasu rika shigowa kasar domin ci rani. A lokacin da take ci gaba da wannan rahoto jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“Kimanin kashi 60% na bakin hauren Afurka su dubu 27 da suka kutsa kai zuwa kasar Spain a wannan shekarar sun fito ne daga kasar Senegal. Kuma ko da yake kasar ta Spain ta cimma yarjejeniyar mayar da wadannan bakin haure zuwa gida, amma ita sabuwar daidaituwar da aka samu game da bai wa Senegal wani kaso na ‘yan kaka-gida da zasu iya shigowa Spain domin ci rani wani babban ci gaba ne a kokarin da ake yi na shawo kan wannan matsala dake dada yin tsamari kusan a kowace rana. To sai dai kuma a daya bangaren su kansu ainifin talakawa dake cikin hali na kaka-nika-yi ba zasu ci gajiyar lamarin ba, saboda yarjejeniyar ta shafi ‘yan wasan motsa jiki ne da masana da ‘yan kasuwa da makamantansu.”

Ita kuwa jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta yi nazari ne akan wata sabuwar barazana da kasashen ACP da suka hada da Afurka da Karibiya da kuma Pacific suke fuskanta dangane da manufofin nan na sassaucin dangaktakar ciniki. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

“A dai halin da ake ciki yanzu kasashen ACP ba su da wani kakkarfan matsayi da zasu iya shiga wata tserereniya ta ciniki da takwarorinsu kasashen Turai dake da ci gaban masana’antu kuma a yanzun suna fuskantar wata sabuwar barazana a karkashin manufofin gamayyar ciniki ta duniya WTO, wadda take ba da fifiko ga sassaucin ciniki. A karkashin kudurin gamayyar wajibi ne a kawo karshen alfarmar da kasashen ACP ke samu daga kungiyar tarayyar Turai wajen shigo da kayayyakinsu a kasuwannin kungiyar da kuma taimako daga gareta tun daga karshen shekara ta 2007, inda ake bukatar ganin kasashen ACP sun bude dukkan kofofin kasuwanninsu tare da dakatar da tsauraran ka’idoji na kwasta domin ba wa kamfanonin Turai shigar da kayayyakinsu a kasashen.”

A cikin wani nazari da tayi jaridar DIE WELT ta lura da cewar wajibi ne a bi diddigin al’amuran Zimbabwe domin kuwa duk wani tashin hankalin da ka taso a wannan kasa zai iya zama ruwan dare ya rutsa da sauran kasashen dake makobtaka da ita. Jaridar ta ce ko da yake a yanzu matsalolin Zimbabwe da barazanar rushewar da kasar ke fuskanta baya da tasiri akan ATK saboda akasarin masu barin kasar lauyoyi ne da injiniyoyi da sauran kwararrun ma’aikata. Amma fa al’amura na iya canzawa a cikin kiftawa da Bisimilla inda za a samu duddab daruruwan ‘yan kudun hijira, wanda lamari ne da zai yi mummunan tasiri akan sauran kasashen kudancin Afurka.