1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

October 20, 2006

Dangantakar kasashen Afurka da China na daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPa

A wannan makon mai karewa jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al’amuran nahiyarmu ta Afurka. Amma da farko zamu fara ne da sharhin jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG akan shirin taimakon nahiyar Afurka da gwamnatin Jamus ta tanadar dangane da shugabancinta ga gamayyar kasashen G8 da suka fi ci gaban masana’antu a duniya tun daga daya ga watan fabarairu mai zuwa. Jaridar dai ci gaba tayi da cewar:

“Shugabar gwamnati Angela Merkel na fatan bai wa taron kolin kasashen G8 da za a gudanar a Jamus watan yuni mai zuwa taken:”Bunkasar tattalin arziki da halin sanin ya kamata”, domin janyo hankali ga duba al’amuran Afurka da idanun basira. Babbar manufarta shi ne a bai wa dangantakar kasashen Afurka da kasashen dake da ci gaban masana’antu wani sabon fasali da zai taimaka kasashen na Afurka su kara karfafa mulkin demokradiyya da yakar cin hanci da kuma kamanta adalci a harkokin yau da kullum.”

To sai dai kuma duk da wannan kyakkyawar niyyar da shugabar gwamnatin Jamus ta nunar, amma bisa ga ra’ayin jaridar BERLINER ZEITUNG kasashen Turai na fuskantar barazanar zama ‘yan rakiya ga kasar China a nahiyar Afurka dake makobtaka da su. Jaridar ta kara da cewar:

“A yayinda kasashen Turai suka yi ko oho da al’amuran Afurka mai makobtaka da su, ita kasar China ta ankara ne da muhimmancin wannan nahiya tana kuma bakin kokarinta wajen cike gibin da ya samu bayan kawo karshen yakin cacar baka tsakanin kasashen yammaci da na gabacin Turai. A halin yanzu haka kasar ta China abin da ya hada da gwamnatinta da kuma ‘yan kasuwarta dake zaman kansu tuni suka tashi gadan-gadan wajen zuba jari a duk fadin nahiyar Afurka. Nahiyar Turai ta fara nadama a game da watsi da tayi da Afurka tana mai danganta nahiyar da yunwa da yake-yake da kuma annoba iri daban-daban. Wannan nadamar kuwa ka iya zama ihu bayan hari nan gaba.”

Ita kuwa jaridar NEUES DEUTSCHLAND tana tattare ne da ra’ayin cewar yarjejeniyar nan ta sassaucin ciniki tsakanin kasashen Turai da na Afurka da Karibiya da Facific ba zata tsinana wa kasashen Afurka kome ba illa ma ta kara jefa su cikin mawuyacin hali na kaka nika yi da kuma sake mayar da hannun agogo baya dangane da nasarorin da wadannan kasashe suka cimma sakamakon tsauraran matakai na tsuke bakin aljifu da suka saba dauka a zamanin baya.

A taron da ya gudanar a Addis Ababan Ethiopiya kwamitin sulhu na kungiyar tarayyar Afurka a wannan makon ya amince da ta kara wa’adin mulkin shugaba Gbagbo na kasar Cote d’Ivoire har ya zuwa 31 ga watan otoban shekara ta 2007. A lokacin da take gabatar da sharhi akan haka jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

“Wani abin lura dai a nan shi ne a baya ga karin wa’adin shugabancin Gbagbo, shi ma P/Mn wucin gadi Charles Konan Banny an kara masa wa’adin watanni goma sha biyu, a yayinda aka maye gurbin tsofon mai shiga tsakani don sasantawa Thabo Mbeki na ATK da shugaban Kongo Brazaville Sassou Nguessou. Amma bukatar da kungiyar tayi na bai wa P/M Banny cikakken iko ga alamu ba zata yiwu ba saboda lamarin ya saba da daftarin tsarin mulkin kasar Cote d’Ivoire. Bugu da kari kuma shugaba Gbagbo ne ke da iko akan sojojin kasar, inda shi kansa hafsan hafsoshin sojan Cote d’Ivoire Phillipe Mangou baya biyayya ga umarnin ministan tsaro sai na shugaban kasa kawai.”