Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 17.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Taron MDD akan yanayi a Nairobin Kenya na daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin Jamus

Masu zanga-zangar adawa da matsalar dimamar yanayi

Masu zanga-zangar adawa da matsalar dimamar yanayi

Taron kare yanayi da aka gabatar a Nairobin Kenya na daya daga cikin muhimman batutuwan Afurka da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus a wannan makon mai karewa, inda jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta ambaci babban sakataren MDD Kofi Annan na mai korafi a game da rashin kyakkyawar niyya daga bangaren kasashe masu ci gaban masana’antu na dakatar da matsalar dimamar yanayi sakamakon hayakin masana’antu mai guba da suke fitarwa zuwa sararin samaniya. Jaridar ta kara da cewar:

“Babbar uammal’aba’isin rashin samun ci gaban kuwa ita ce kasar Amurka wadda ke fatali da yarjejeniyar kare makomar yanayi ta Kyoto, wadda a cikinta gaggan kasashe 35 dake da ci gaban masana’antu suka yi alkawarin kayyade yawan hayaki mai guba da suke fitarwa zuwa sararin samaniya nan da shekara ta 2012. Su ma kasashe masu matsakaicin ci gaban masana’antu irinsu China da Brazil suna koburus da manufofin yarjejeniyar. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba a game da korafin da Kofi Annan yake yi saboda ci gaban dimamar yanayin zai kara tsaurara matsalar fari a sassa da dama na nahiyar Afurka.”

Ita ma jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU tayi bitar matsalar dimamar yanayin inda ta ce Afurka ce tafi jin radadin wannan mummunan ci gaba. Jaridar dai sai ta kara da cewar:

“Alkaluma na baya-bayan nan sun nuna cewar nahiyar Afurka dake kunshi da kashi daya bisa biyar na al’umar duniya ita ce zata fi fama da radadin mummunan tasirin dimamar yanayin da ake fuskanta. A baya ga matsalar fari, nahiyar kazalika zata sha fama da ambaliyar ruwa a yankunanta na kurmi dake yammaci tare da koma bayan amfanin gona. A wannan karnin da muke ciki kawai an yi hasashen cewar sama da mutane miliyan 180 zasu sha fama da radadin dimamar yanayin a nahiyar Afurka.”

A mayar da martani akan fafatawar da ake yi yau sama da tsawon makonni biyu tsakanin Larabawan Janjaweed da bakar fata a yankin dake kusa da yankin iyakar kasarta, gwamnatin Chadi ta kafa dokar tabaci a sassa daban-daban na kasar. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG tayi bitar matsalar inda take cewar:

“Ta la’akari da rikici mai kama da yakin basasa da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin iyaka tsakanin Chadi da Sudan an fara hakikancewa cewar fargabar yaduwar rikicin lardin Darfur zuwa kasashen Chadi da Janhuriyar Afurka ta Tsakiya ta fara tabbatuwa. Yau kimanin shekara daya ke nan da shugaban kasar Chadi Iriss Deby ke bakin kokarinsa wajen mayar da martani akan hare-haren ‘yan tawaye, wadanda ke shirya matakansu daga harabar Sudan kuma gwamnati a fadar mulki ta N’Djamena ke kyautata zaton cewar suna samun goyan baya ne daga gwamnatin Sudan. Ita kuwa janhuriyar Afurka ta Tsakiya tun abin da ya kama daga wajejen karshen watan oktoban da ya gabata ne take fama da hare-haren ‘yan tawaye, wadanda su ma bisa ga dukkannin alamu fadar mulki ta Khartoum ce ke mara musu baya. Dukkan rikice-rikicen yankin dai suna da alaka da juna kuma Sudan ita ce ummal’aba’isinsu.”

Kasar Cote d’Ivoire, kamar yadda jaridar DIE TAGESZEITUNG ta nunar, har yau tana lalube ne a cikin dufu a fafutukar neman zaman lafiya da shirya sahihin zabe na demokradiyya duk kuwa da kudurori masu yawa da kungiyar tarayyar Afurka da MDD suka zartas. Ba kuwa kowa ne ke hana ruwa gudu ba illa shugaba Gbagbo da P/M Banny, a yayinda su kuma al’umar kasar suka fara kosawa da mawuyacin halin da suka samu kansu a ciki sakamakon yakin basasar kasar dan shekaru biyar. Shi dai Gbagbo a halin yanzu sai dada nanatawa yake yi cewar wai su kansu ‘yan kasar ne ke da ikon warware rikicinsu, to amma bai fito fili ya fayyace ainifin makasudinsa game da haka ba.