Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 01.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a lardin Darfur shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus

Darfur

Darfur

Mawuyacin halin da ake ciki a lardin Darfur na kasar Sudan na daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon, musamman ma gazawar da hukumar kula da hakkin dan-Adam ta MDD tayi dangane da mayar da martani akan wannan mawuyacin hali kuma akan haka jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG take cewar:

“Duk da mawuyacin hali na jinkai da ake ciki a lardin Darfur din kasar Sudan, amma hukumar MDD akan hakkin dan-Adam ta kasa mayar da martanin da ya dace da lamarin da kuma kalubalantar fadar mulki ta Khartoum. A sakamakon haka shi kansa sakatare-janar na MDD Kofi Annan yayi kiran gudanar da wani zama na gangami akan lardin na Darfur yana mai samun goyan baya daga kasashen Jamus da Faransa da Kanada da kuma Birtaniya.”

To sai dai kuma duk da wannan goyan bayan da ita Jamus ta bayar ga shawarar gudanar da wani zama na gangami akan lardin Darfur, wasu daga cikin wakilan ‘yan Christian Union dake da hannu a gwamnatin hadin guiwa sun bayyana rashin jin dadinsu a game da tayi da ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung yayi a game da tura sojojin kasar domin aikin kiyaye zaman lafiya a Darfur. Jaridar SÜDDEUTSVHE ZEITUNG ta yi bitar lamarin ta kuma ci gaba da bayani tana mai cewar:

“A dai halin da ake ciki yanzu haka Jamus na da sojojinta 275 a kasar Sudan, inda a lardin Darfur take taimakawa da jiragen sama na dako domin sojan kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afurka ta AU dake yankin. A saboda haka babu wani takamaiman dalilin tura wasu sojojin na kasa zuwa Darfur. Bugu da kari kuma shi kansa shugaba Omar Hasan Al-Bashir ya bayyana kyamar ganin wani soja da ba na kungiyar tarayyar Afurka ba a harabar kasarsa. A baya ga haka ko da ma an tsayar da shawarar tura sojoji na ketare, ita kanta Kungiyar Tarayyar Afurka, har ma da MDD duk sun sani cewar babu wata kasa ta Turai da zata yarda ta tura sojojinta zuwa lardin na Darfur.”

A can kasashen Chadi da Janhuriyar Afurka ta Tsakiya ana fuskantar kazamar ta’asa, inda kungiyoyin kare hakkin dan-Adam ke zargin gwamnatin kasar Afurka ta Tsakiyar mai samun goyan bayan Faransa da laifin tafiyar da wani yaki na kare dangi, in ji jaridar DIE TAGESZEITUNG. Jaridar ta kara da cewar:

“A kasashen Chadi da Janhuriyar Afurka ta Tsakiya, ba kawai ‘yan tawaye masu daurin gindin fadar mulkin Khartoum ne kadai ke aikata ta’asa ba hatta su kansu gwamnatocin kasashen biyu na da hannu dumu-dumu wajen keta hakkin dan-Adam. A kasar Chadi, kamar yadda rahotanni suka nunar, jami’an gwamnati na ba da goyan baya ga wata kungiyar sa kai ta tsaron kai bisa manufofi na kabilanci a gabacin kasar. Wannan kungiya ta kan kai hare-harenta ne akan Larabawa dake zaune a yankin da kuma wadanda ke lardin Darfur. Dangane da Janhuriyar Afurka ta Tsakiya kuwa gwamnati ce ke farautar ‘yan hamayya da farar fula da ma sojoji wadanda ke da nasaba da kabilun shuagabannin ‘yan tawaye.”

A wannan makon ne wa’adin aikin tsaron zaman lafiya na sojan Jamus da sauran kasashen Turai ya kawo karshensa a kasar Kongo. Jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi amfani da wannan dama domin duba halin da kasar ke ciki da kuma abin da ka biyo bayan janyewar sojojin na Eufor daga kasar, inda ta ce:

“A dai halin da ake ciki yanzun ba wanda zai iya hasashen makomar kasar Kongo bayan shekaru masu yawa da tayi a karkashin danyyen mulki na kama karya da kuma yakin basasar da ya biyo baya. Akwai barazana iri-iri da kasar ke fuskanta. Shi kansa zaben da aka gudanar ya bayyanar a fili yadda kasar ta rarrabu, inda mazauna yammacinta suka ba wa Bemba goyan baya sannan su kuma ‘yan gabaci suka rufa wa Kabila baya. Ta la’akari da haka bai kamata duniya tayi zaton cewar bayan wannan zabe bata da sauran alhaki da ya rataya wuyanta dangane da makomar kasar ta Kongo. Wajibi ne a yi duk bakin kokari domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyxar hankali a wannan yanki baki daya.”