1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

December 9, 2006

Har yau dai rikicin lardin Darfur na ci gaba da daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPU

Da farko dai zamu leka ne zuwa kasar Kongo, inda a wannan makon aka rantsar da shugaba Joseph Kabila a matsayin zababben shugaban wannan kasa tare da halarcin shuagabannin Afurka da dama. Jaridar FRANKFURTER ALGEMEINE ZEITUNG tayi bayani akan haka tana mai cewar:

“Joseph Kabila mai shekaru 35 da haifuwa, ba ma kawai shi ne mafi kankantar shekaru tsakanin shuagabannin Afurka ba, kazalika shi ne na farko da aka nada sakamakon zabe na demokradiyya as kasar Kongo tun bayan samun ‘yancin kanta daga Turawan belgium a shekara ta 1960.”

Ita ma jaridar BERLINER ZEITUNG tayi bitar wannan ci gaba inda take saka ayar tambaya a game da makomar kasar ta Kongo. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

“Babban abin da al’umar Kongo ke fatan gani daga sabon shugabansu Joseph Kabila shi ne ya bai wa kamfanonin ketare damar zuba jari a kasar ba tare da magudi ko cin hanci ba. Wadannan kamfanoni suna iya zuba dubban miliyoyi a harkar hakar ma’adinai da sauran bangarori masu muhimmanci ga tattalin arzikin kasar Kongo, ita kuma a nata bangaren gwamnati ka iya amfani da kudaden harajin da zasu kwarara zuwa baitul-malinta daga wadannan kamfanoni domin kyautata hanyoyin sadarwa a duk fadin kasar ba tare da la’akari da wata manufa ta kabilanci ba.”

Ita ma maganar lardin Darfur ta dauki hankalin jaridun na Jamus a wannan makon, inda jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ke batu a game da barazanar yaduwar rikicin domin mamaye yankin gaba daya. Jaridar ta ce:

“Wani abin dake kara tsaurara rikicin da ake fama da shi a lardin Darfur, wanda kuma ke barazanar hadawa da kasashen Chadi da janhuriyar Afurka ta tsakiya shi ne gwagwarmayar yada angizo tsakanin wasu daga cikin shuagabannin kasashjen yankin. Wannan maganar musamman ta shafi shugaban Libiya Mu’ammar Ghaddafi, wanda shi ne ya rufa wa Idris Deby da Omar Al-Bashir baya wajen kwatar mulkin kasashensu a zamanin baya. A halin yanzu haka akwai wasu bayanan dake nuna cewar Libiya tana ba da taimakon kudi ga Larabawan Janjaweed a Sudan da kuma kungiyoyin tawayen kasar Chadi.”

A karshen makon da ya wuce wasu ‘yan Afurka dake kaka-gida a nan Jamus suka gudanar da wani taron bita akan manufofin raya kasa, wadanda suka ce ba su tsinana wa nahiyar kome ba a cikin shekaru 60 din da suka wuce suna masu neman ganin an canza akalar manufofin domin dora su akan wata turba ta kawance. Jaridar GENERAL-ANZEIGER da ta tura wakilinta zuwa zauren taron ta ambaci daya daga cikin mahalarta zauren yana mai cewar:

“A duk inda aka samu ci gaba, idan an lura za a ga hakan ya faru ne ta hanyar taimakon kai da kai, misali a Botswana ko Mauritius. Wannan na mai yin nuni ne da cewar matsalar ta talauci, matsala ce da za a iya tinkararta, amma ba a zauna sasakai a rungumi kaddara ba. Dukkan taimakon raya kasar da ake bayarwa sun kasance masu yin cikas ga matakan garambawul da kasashen Afurka ke bukata domin daga matsayin rayuwar al’ummominsu.”