Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 15.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a gabacin Afurka shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon

Mayakan Kotunan Musulmi a Somaliya

Mayakan Kotunan Musulmi a Somaliya

Da farko shirin zai fara ya da zango ne a can yankin gabacin Afurka inda ake fama da rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa, wanda kuma in ba tashi tsaye aka yi aka magance shi ba zai kara jefa wannan yanki cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi. Wannan maganar musamman ta fi shafar kasar Somaliya, wadda tayi shekara da shekaru bata da wata halastacciyar gwamnati, sannan ita kuma gwamnatin wucin gadin dake da mazauninta a Baidoa bata da wani angizo na a zo a gani. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi bitar matsalar inda take cewa:

„Tun abin da ya kama daga watan yunin da ya wuce gamayyar kotunan Musulmi ta kasar Somaliya ta tabbatar da ikonta a birnin Mogadishu, sannan dakarunta kuma suka tinkari Baidoa domin mamayar birnin da fatattakar gwamnatin wucin gadin dake da mazauninta a can. Amma fa kungiyar ba ita ce kadai ke da iko a Mogadishu ba. Domin kuwa tana samun goyan baya na dakaru da makamai daga Eritrea, kasar da ba ta ga maciji da Habasha. Ita kuma Habasha nata bangaren ta sha kokawa a game da cewar masu rike da madafun iko a Mogadishu na tallafa wa Somaliyawan Ogaden dake gabacin kasar ta Habasha. A dai halin da ake ciki yanzu ba wanda ya san ainifin bakin zaren warware wannan rikici.”

An fara hangen yiwuwar yin katsalandan a lardin Darfur na kasar sudan, inda kasashen Amurka da Birtaniya suka bayyana goyan bayansu da a kebe wasu yankunan lardin da za a haramta shawagin jiragen saman yakin Sudan a cikinsu ita kuma MDD ta tura jami’an bin bahasi zuwa lardun na Darfur domin tantance halin da ake ciki. A lokacin da take rawaito wannan rahoton jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“A wannan bangaren ana fatan samun hadin kai da kasar Faransa, wadda ke da sojojinta a makobciyar kasa ta Chadi. Tuni dai Amurka tayi kira ga Sudan da ta amince da tsugunar da sojan kiyaye zaman lafiya na MDD a Darfur kuma mai yiwuwa lamarin ya kai ga kayyade wa kasar ta Sudan wa’adin amincewar in kuwa ba haka ba ta fuskanci matakai na sojabisa manufa.”

A wannan makon wasu kasashe 15 na Afurka suka hallara a Nairobin Kenya domin gudanar da taro akan al’amuran tsaro da zaman lafiya da kuma raya makomar kasa a yankunan manyan tafkunan dake kuryar nahiyar. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta gabatar da rahoto akan taron tana mai cewar:

“Yankin manyan tafkunan Afurka tamkar wata taska ce ta dimbim arzikin da Allah Ya fuwace wa nahiyar, amma kuma a nan ne aka fi fama da rikici. Kimanin mutane miliyan hudu suka mutu sannan wasu miliyoyin kuma suka tagayyara sakamakon yake-yake tsakanin kasashen yankin da kuma yake-yake na basasa a cikin shekaru 15 da suka wuce. Ko shakka babu kuwa kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma China dake halartar taron ta bayan fage na da hannu dumu-dumu a wadannan rikice-rikice da suka ki ci suka ki cinyewa.”

A karshen watan da ya gabata ne sojan kiyaye zaman lafiya na KTT suka kammala aikinsu a kasar Kongo. Jaridar DIE WELT tayi amfani da wannan dama wajen neman bayani daga babban kwamandan sojojin Karlheinz Viereck a game da nasarar aikin nasu. Ga dai abin da yake cewa:

“Ko shakka babu aikin yayi nasara matuka ainun, kuma ba abin da ya raghe a yanzun illa a kwashe sojojin su kimanin 800 daga Kinshasa da kuma wasu 1200 dake Gabun domin dawo da su gida. Za kammala kwashe sojojin baki daya nan da karshen watan janairu mai zuwa. A takaice kyakkyawan hadin kai da aka samu tsakanin sojojin na Eufor da na MDD ya taimaka aka hana billar tashe-tashen hankula kuma maganar yakin basasa jita-jita ce kawai, ba wani takamaiman dalilin dake yin nuni ga haka.”