Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 19.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a Somaliya shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus game da batutuwan Afurka a wannan makon

Mogadishu

Mogadishu

A wannan makon dai babban abin da ya fi daukar hankalin jaridun na Jamus a rahotannin da suka gabatar dangane da al’amuran Afurka shi ne a halin da ake ciki a Somalia. Amma da farko zamu duba rahoton da jaridar DIE TAGESZEITUNG ta rubuta a game da halin da ake ciki a Lardin Darfur na kasar Sudan, inda a wannan makon MDD ta fara gabatar da taimakon kayan aiki ga rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen Afurka, amma a daya hannun ake ci gaba da kisan kiyashi a wannan lardi, kamar ysadda jaridar ta rawaito ta kuma kara da cewar:

“A daidai lokacin da MDD ta fara gabatar da matakinta na mara wa sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashen Afurka da kayan aiki a lardin Darfur gwamnati a fadar mulki ta Khartoum ta ba da sanarwa cewar wai a makon jiya mutane sama da metan sun halaka sakamakon rigingimu na kabilanci tsakanin makiyaya na Habaniya da Falata, amma tuni ta tura wakilai domin shiga tsakani don sasantawa. Gwamnatin Sudan dai ya sha fakewa da ire-iren wannan ikirarin a rufa-rufa a game da ainifin abin dake faruwa a lardin Darfur, inda daruruwan mutane suka mutu sannan aka fatattaki wasu miliyoyin a cikin shekaru hudun da suka wuce.”

Shugaban rikon kwarya na kasar Somalia Abdulklahi Yusuf na fatan ganin kasarsa ta shiga wani sabon yanayi na zaman lafiya da klwanciyar hankali, amma fa bisa ga dukkan alamu al’umar kasar, musamman mazauna fadar mulki ta Mogadishu basa kaunar ganin an kwace damararsu ta makamai. A lokacin da take bitar wannan mawuyacin hali da ake ciki jaridar Financial Times ta Jamus cewa tayi:

“Tun bayan da shugaban gwamnatin rikon kwarya Abdullahi Yusuf ya mayar da mazauninsa zuwa Mogadishu mako daya da ya wuce ake fama da musayar wuta kusan a kowace rana ta Allah a fadar mulkin ta Somaliya. Wani abin mamaki ma shi ne yadda aka rika jin rugugin harsasai a daidai lokacin da shugaban ke ganawa da tsaffin shuagabannin kungiyoyin da basa ga maciji da juna a Mogadishu akan manufar kwance damarar makaman dakarunsu. Bisa ga dukkan alamu dai shugaban baya da cikakken goyan baya, inda aka ji wani daga cikin tsaffin mazauna Mogadishu na cewar duk da kyamar musulmi masu zazzafan ra’ayin akida da ake yi, su ne kadai suka samu ikon tabbatar da kwanciyar hankali a birnin.”

Ita kuwa jaridar NEUES DEUTSCHLAND tayi bita ne akan taron duniya akan kyautata makomar zamantakewa a Nairobin Kenya inda take cewar:

“Tun bayan da aka gabatar da taron a Porto Alegre a shekara ta 2001 ya zuwa yanzu babu wata takamaimiyar nasarar da aka cimma illa ci gaba da bayyana fata na gari. Bugu da kari kuma akwai masu korafi a game da yadda gaggan kungiyoyi masu zaman kansu ke babakere a lamarin ba tare da wani takamaiman shirin aiki bisa manufa ba. Amma fa a hakika gabatar da shi kansa wannan taro babban ci gaba ne a kokarin kyautata jin dadin makomar rayuwar dan-Adam a doron kasa.”

Kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya ta samu sabon mai koyar da ‘yan wasanta, tsofon mai koyar da ‘yan wasan kasar Jamus Berti Vogts, wanda zai kama aikinsa a watan maris mai zuwa. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG tayi hira da shi, inda ta tambaye shi ko shin mene ne dalilinsa game da amincewa da aikin a Nijeriya? Sai Vogts ya ce:

“A hakika ko yar da ‘yan wasan Afurka abin mafirin ciki ne da murna, musamman a wasanninsu na share fage domin shiga gasannin cin kofunan Afurka da na duniya. A halin yanzu haka kungiyoyin wasannin na kasashen Afurka duk sun dokata a game da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a ATK. Na san kungiyar wasan ta Nijeriya saboda mun kara da ita matsayinta na mai koyar da kungiyar wasan Jamus da kungiyar wasan Scottland. Akasarin ‘yan wasanta suna wasa ne a Turai. A saboda haka muhimmin abu a yanzu shi ne a hada kansu su zama tamkar tsintsiya madaurinki daya.”