1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

January 26, 2007

Taron duniya akan zamantakewa a Nairobin Kenya shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPP
Taron duniya akan zamantakewa a Nairobi
Taron duniya akan zamantakewa a NairobiHoto: AP

Muhimmin abin da ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon mai karewa shi ne taron duniya akan zamantakewar da aka gudanar a Nairobin Kenya da kuma manufofin China dangane da kasashen Afurka…Amma da farko zamu fara ne da duba mawuyacin halin da ake fama da shi a kasar Guinea. Ba kuma tare da wata-wata ba zamu zarce ga rahoton jaridar DIE TAGESZEITUNG dangane da taron duniya akan zamantakewar da aka gudanar a Nairobin Kenya, inda take tattare da ra’ayin cewar Afurka ta amfana da wannan taro. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Kungiyoyin fafutukar kyautata makomar jin dadin jama’a a nahiyar Afurka sun yi amfani da wannan taro domin yayata manufofinta na adawa da shirin yarjejeniyar cinikin da ake da niyyar gabatarwa tsakanin nahiyar da Kungiyar Tarayyar Turai, inda aka fuskanci cincirindon kungiyoyi na kasashen Turai dake neman ganin an dama da su a wannan mataki. Kazalika nan gaba gwamnatocin nahiyar Afurka ba zasu samu damar cin karensu babu babbaka, kamar yadda suka saba a zamanin baya ba, domin kuwa al’umar kasashensu zasu rika ta da kayar baya su dinga shiga zanga-zangar adawa da duk wani mataki na gwamnati da zai yi cikas ga makomar jin dadin rayuwarsu.”

To babban misali a nan dai shi ne halin da ake ciki na gwagwarmayar kama madafun iko a kasar Guinea ta yammacin Afurka, inda ‘yan adawa suka dage akan cewar lalle sai shugaba Lansana Conte mai fama da rashin koshin lafiya yayi murabus. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“Kungiyoyin kwadago na kasar Guinea na dora wa shugaba Lansana Conte alhakin mawuyacin hali na tabarbarewar al’amuran rayuwa da al’umar Guinea suka dade suna fama da shi. Da yawa daga manazarta na tattare da ra’ayin cewar shugaban mai fama da rashin koshin lafiya ba ya da wani tasiri a al’amuran kasar mai yawan mutane miliyan tara, wadda kuma tattalin arzikinta ke dada tabarbarewa sakamakon cin hanci dake dada zama ruwan dare.”

Kasar China, a zamanin baya-bayan nan sai kara kutsa kai take yi a nahiyar Afurka, inda a watan nuwamban bara ta hada taron koli tsakaninta da kasashen nahiyar a birnin Beijing kuma a halin yanzu haka shugaba Hu Jintao na kan bulaguron da zata kai shi kasashe takwas na wannan nahiya. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka na dari-dari da gagarumin mataki na diplomasiyya da tattalin arziki da China ke dauka a manufofinta dangane da nahiyar Afurka. Babban abin dake ci musu tuwo a kwarya dai shi ne yadda Chinar ke tafiyar da huldar ciniki da zuba jari da kuma gabatar da taimako ba tare da ta gindaya wani sharadi ba. A ra’ayinsu hakan babban cikas ne ga kokarin da suke na tabbatar da mulkin demokradiyya a nahiyar Afurka.”

Har yau ana ci gaba da fama da mace-macen ‘yan gudun hijira dake amfani da kwale-kwale tun daga gabar tekun Senegal domin karasowa zuwa nahiyar Turai. Mujallar Stern tayi bitar matsalar dangane da wasu mutane 105 da suka halaka a teku sakamakon yunwa da kishirwa. Mujallar ta ce kowane daga cikin mutanen su 105 sai da ya biya kudin CFA dubu 250, wato kwatankwacin Euro 400.