Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 02.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Tabargazar cin hancin da ake zargin kamfanin Siemen ta aikatawa a Nijeriya na daya daga cikin muhimman rahotannin jaridun Jamus

A tabargazar cin hanci da ake zargin kamfanin Siemens da aikatawa an gano cewar tana da hannu dumu-dumu a harkar ba da toshiyar baki a Nijeriya. A kuma wannan makon shugaban kasar China Hu Jintao ya fara bulaguron nahiyar Afurka..Wadannan wasu ke nan daga cikin muhimman rahotannin da jaridun Jamus suka mayar da hankali akansu dangane da nahiyar Afurka.

Ana zargin kamfanin Siemens da laifuka na tabargazar mara wa cin hanci baya a Nijeriya a zamanin mulkin marigayi janar Sani Abacha. Jaridar SÜDDEUTSCHE Zeitung ta gabatar da rahoto akan haka inda take cewar:

“An gano a rubuce cewar a cikin shekarun 1990 kamfanin Siemens ta tura miliyoyi na dalar Amurka zuwa ga ajiyan bankunan ministoci da gaggan jami’an hukumar Nitel ta Nijeriya. Gaba daya sama da mutane 100 suka ci gajiyar wadannan kudade na cin hanci. Shi kansa shugaban kasa na wancan lokaci janar Sani Abacha sai da aka ba shi toshiyar baka. Bincike ya nuna cewar kamfanin na Siemens kan kashe abin da ya kai Euro miliyan goma na toshiyar baki a Nijeriyar a duk shekara, kuma bayan da ta dakatar da biyan wadannan kudade sai aka hana mata kwangila.”

A wannan makon shugaban kasar China Hu Jintao ya fara Bulaguron kasashen Afurka da suka hada da Kamaru da Liberiya da Zambiya da Namibiya da Sudan da Afurka ta Kudu hade da Seychells da Muzambik. Amma duk wanda yayi bitar wannan ziyara zai ga an zabi wadannan kasashe ne dangane da albarkatun kasar da Allah Ya fuwace musu. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

“A karo na biyu a cikin watanni 12 kacal shugaban kasar China Hu Jintao ya kai ziyara kasashen Afurka. Kamar a wancan lokaci a wannan karon ma yana dauke da abin da ya kai dala miliyan dubu uku na taimako ga kasashen Afurka. Kasar ta China tayi alkawarin gabatar da rancen kudui mai rafusa ga kasashen Afurka a cikin shekaru uku masu zuwa, a baya ga alkawarin da tayi wa kasashen na ribanya yawan taimakonta na raya kasa har sau biyu nan da shekara ta 2009. Amma fa hakan ba wata alama ce ta so da kauna ga kasashen Afurka ba. Duk wanda yayi bitar lamarin da idanun basira zai ga cewar ainifin maslaharta ne ta sa gaba. Domin kuwa a wannan karon daidai da ziyarar farko da shugaba Hu Jintao ya kai ga Afurka wasu kebabbun kasashen da Allah Ya albarkace su da danyyun kayayyaki ne ya ke kai wa ziyarar.”

Yara na fuskantar mummunar barazana a lardin Darfur dake yammacin kasar Sudan. Jaridar DER TAGESSPIEGEL tayi nazari akan haka inda take cewar:

“Kimanin kashi 75 cikin dari na ‘yan gudun hijirar dake Darfur da kuma wadanda ke sansanonin ‘yan gudun hijira a Chadi mata ne da yara kanana, kuma sai dada shiga hali na kaka-nika-yi suke yi. Domin kuwa a ‘yan makonnin baya-bayan nan ana sha fuskantar farmaki da sace-sacen mutane da kuma dauki ba dadi a lardin Darfur ta yadda ita kanta hada-hadar taimako ta kasa da kasa take fuskantar barazanar tabarbarewa. Asusun taimakon yara na MDD ya ce a halin yanzu haka yara kimanin miliyan biyu ke cikin hadari game da makomar rayuwarsu sakamakon kara tabarbarewar halin da ake ciki. Bisa ga ra’ayin ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul a yanzu lokaci yayi da za a tura karin sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa yankin sannan ita kuma MDD ta saka takunkumin haramcin sayarwa da kasar Sudan makamai.”