Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Amurka na shirin kafa cibiyar sojinta a nahiyar Afurka. A kuma halin da ake ciki yanzu an samu raguwar yawan sojoji yara a nahiyar ta Afurka.

Maganar sojoji yara da shirin Amurka game da samar da wata tsayayyar cibiya ta sojanta a nahiyar Afurka na daga cikin muhimman batutuwan da suka mamaye kanun rahotannin jaridun Jamus akan al’amuran Afurka a wannan makon. Amma da farko zamu fara ya da zango ne a Zimbabwe domin duba mawuyacin hali na rayuwa da talakawan kasar ke ciki, inda datti ya mamaye yankunan ‘yan rabbana ka wadata mu, wadanda kuma ke fama da yaduwar cutar kwalera. Jaridar DIE WELT ce take ba da wannan rahoton ta kuma kara da cewar:

“Sakamakon binciken da aka gudanar ya nuna cewar kimanin kashi 46% na illahirin mazauna wani yanki na ‘yan rabbana ka wadatamu da ake kira Mabare na fama da karayar zuci yanzu haka. Kasar Zimbabwe wadda har ya zuwa wasu ‘yan tsirarun shekaru da suka wuce take fitar da abinci zuwa ketare, a yau ta wayi gari tana fama da hauhawar farashin kaya da misalin kashi 1281 a cikin dari da koma bayan tattalin arziki na kashi 50 a baya ga wasu kashi 80 cikin dari na al’umarta dake zama hannu baka-hannu-kwarya.”

An samun raguwar sojoji yara a nahiyar Afurka bayan shekara da shekarun da aka yi ana amfani da su a yake-yake na basasa a kasashe daban-daban na nahiyar. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta gabatar da rahoto tana mai cewar:

“An yi shekaru da dama ana danganta matsalar sojojin yara da rikice-rikice a nahiyar Afurka duk da cewar yawan yaran da ake amfani da su a rikice-rikice a nahiyar Asiya da Latin Amurka bai gaza na Afurka ba. A kuma halin da ake ciki yanzu an samu kyakkyawan ci gaba, inda in banda a kasashe kamarsu Cote d’Ivoire da arewacin Uganda, an samu raguwar sojoji yara kanana a nahiyar Afurka. To sai dai kuma hakan ya samu ne sakamakon kawo karshen wasu daga cikin manyan rikice-rikice na nahiyar, amma ba saboda halin sanin ya kamata na masu alhakin amfani da yaran ba.”

Kasar Amurka ta tsayar da shawarar samar da wata tsayayyar cibiya ta rundunar sojanta a nahiyar Afurka. To sai dai kuma a halin yanzu daga birnin Stuttgart ne za a rika tafiyar da al’amuran sojojin. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta gabatar da rahoto tana mai cewar:

“A cikin wata sanarwar da ya bayar shugaba Goerge W. Bush na Amurka yayi ikirarin cewar wai manufar gwamnatinsa a game da bude wata cibiyar sojan Amurka ta nahiyar Afurka ita ce domin kara tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro a wannan nahiya mai kabilu iri daban-daban. Shirin na Amurka mai taken Africom zai kankama ne tun daga daya ga watan oktoba na shekara mai zuwa.”

Ita kuwa jaridar DIE TAGEZEITUNG a cikin dan takaitaccen sharhin da tayi a game da wannan ci gaba cewa tayi:

“Wannan sanarwar da Amurka ta bayar a daidai lokacin da shugaban kasar China Hu Jintao ke balaguron kasashen Afurka tana mai yin nuni ne da yadda kasar ta Amurka ke kokarin karya alkadarin tasirin da China ke neman yi a Afurka. Ita dai Amurka a yanzu haka tana sayen kashi 10% na mai da take bukata ne daga nahiyar Afurka.”