Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 23.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Mawuyacin hali na zaman dardar da ake ciki a kasar Guinea na daukar hankalin jaridun Jamus

Zaman dardar a Guinea

Zaman dardar a Guinea

A daren larabar da ta shige kwamitin sulhu na MDD ya bai wa kungiyar tarayyar Afurka cikakken ikon tafiyar da aikin tsaron zaman lafiya a kasar Somaliya har tsawon watanni shida masu zuwa. To sai dai kuma kamar yadda jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta lura shirye-shiryen tura sojojin kiyaye zaman lafiyar zuwa Somaliya ba abu ne mai saki ba, domin kuwa kawo yanzun duka-duka kashi 50% na yawan sojojin da ake bukata domin tafiyar da wannan aiki ne ake da tabbaci game da su. Amma jaridar ta ambaci Said Djinnit dan kasar Aljeriya dake da alhakin kula da manufofin kungiyar tarayyar Afurka akan al’amuran tsaro da kiyaye zaman lafiya yana mai bayyana cewar wajibi ne a ba da la’akari da gaskiyar cewar a yanzu ne fa kungiyar, wadda aka kirkirota misalin shekaru hudu da suka wuce ta fara kokarinta na shawo kan rikice-rikicen nahiyar Afurka da kanta ba tare da dogaro akan ketare ba. A saboda haka tilas ne a saurara mata a ga irin rawar da zata taka bisa manufa.

A kasar Muzambik, kimanin mutane dubu 120 ke kan hanyarsu ta neman mafaka sakamakon ambaliyar ruwan da ta rutsa da yankin. To sai dai kuma a wannan karon sai da aka gargade su kafin afkuwar bala’in domin su kasance a cikin shirin in ji jaridar DER TAGESSPIEGEL, wadda ta bayyana mamakinta a game da yadda aka yi ko oho da makomar mutanen da bala’in ya rutsa dasu. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“A misalin shekaru bakwai da suka wuce lokacin da bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da kasar Muzambik tare da sanadiyyar rayukan mutane sama da 700 duk duniya gaba daya aka tashi gadan-gadan domin kai mata doki, amma abin mamaki a yanzun sai ga shi kasar ta sake fuskantar wani bala’i irin shigen wancan, amma an yi ko oho da ita. Abin dai da ya taimaka aka kauce wa tsautsayi irin na shekara ta 2000 shi ne kafar da aka samu ta gabatar da gargadi ga jama’a akan lokaci.”

Tashe-tashen hankula a kasar Guinea na barazana ga yankin yammacin Afurka baki daya, wannan shi ne ra’ayin jaridar FRANKFURTER RUDNSCHAU, bayan da tayi bitar tushen rikicin inda take cewar:

“Musabbabin rikicin shi ne yajib aiki na gama garin da aka shiga a kasar a ranar 10 ga watan janairun da ya wuce. Tarayyar kungiyar kodago ta kasar da jam’iyyun hamayya sun shiga zanga-zangar adawa da mawuyacin hali na rayuwa da jama’a ke ciki da hauhawar farashin kaya da kuma cin hanci da ya zama ruwan dare a duk fadin kasar Guinea, wadda albarkace ta da kashi 50% na yawan ma’adanin Bauxite a duniya baki daya. Duk da albarkatun kasar da Alla Ya fuwace mata, kimanin kashi 40% na al’umar Guinea ke zama hannu-baka-hannu-kwarya. Kasar ma a yanzu ita ce lambawan a fannin cin hanci a nahiyar Afurka. Kuma ana dora laifin wannan mummunan ci gaba ne akan shugaba Lansana Konte dan shekaru 73 dake fama da rashin koshin lafiya. A dai halin yanzu an samu sararawar al’amura sakamakon dokar tabace dake ci, kuma kasar Faransa ta tura jirgin ruwan yakinta domin kwashe baki ‘yan kasashen ketare su dubu 7 in har zarafi ya kama.”

Ita ma jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi bitar halin da ake ciki a kasar Guinea a karkashin wannan doka ta ko-ta-kwana ta soja da shugaba Conte ya kafa, inda take cewar:

“Tun bayan kafa wannan doka jami’an tsaro ke bi gida-gida suna wawason dukiyar jama’a ba gaira ba dalili. A sakamakon matakai na ta’asa da jami’an tsaron ke dauka a birnin Kwanakry mutane na fargabar barin gidajensu. Kuma rahotanni sun bayyana kashe-kashe na gilla daga bangaren mahukunta. A takaice ana fama da rashin doka da oda a wannan kasa, wadda ake fargabar yaduwar rikicinta zuwa kasashen dake makobtaka da ita a yammacin Afurka.”