Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Shari'ar da aka gabatar akan wasu 'yan sandan da ake zarginsu da zama ummal'aba'isin mutuwar wani dan afurka a wakafi na daga cikin abubuwan da jaridu suka yi sharhi akansu

A wannan makon ne aka fara shari’ar wasu ‘yan sandan Jamus guda biyu da ake zarginsu da laifin mutuwar wani fursuna dan Afurka da suka tsare a gidan wakafi misalin shekaru biyu da suka wuce,

A taronsu a birnin Berlin ministocin taimakon raya kasashe masu tasowa na G8 sun a wannan makon sun duba hanyoyin da za a bi a kara inganta manufar zuba jari a kasashen Afurka...Wadannan wasu ke nan daga cikin kanun rahotannin da dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus dangane da batutuwan Afurka a wannan makon mai karewa...

Amma da farko ya zamu fara ne da ya da zango a kasar Zimbabwe, inda a daidai lokacin da kungiyar raya tattalin arzikin kudancin Afurka ke gudanar da taronta a Tanzaniya ‘yan sandan kasar ta Zimbabwe ke ci gaba da daukar matakai na muzanta wa ‘yan hamayya. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“A ranar larabar da ta gabata ‘yan sanda a kasar Zimbabwe sun sake tasa keyar jami’in hamayya Morgan Tsivangirai zuwa gidan wakafi, inda suka tsare shi tsawon sa’o’i da dama. Bayanai sun ce an kame Tsivangirai da wasu abokan aikinsa 20 ne a daidai lokacin da yake gudanar da wani taron manema labarai. A makonni biyun da suka gabata sai da ‘yan sandan Zimbabwe suka tsare jami’in hamayya tare da azabtar da shi har sai da aka kai shi asibiti neman magani. Amma duk da ire-iren ta’asa da muzantawar da ‘yan hamayya ke fuskanta a Zimbabwe mahalarta taron na Tanzaniya sun kasa cimma daidaituwa akan yadda zasu tinkari shugaba Mugabe da wannan matsala.”

A wannan makon aka gabatar da shari’a akan wasu ‘yan sandan Jamus guda biyu a garin Dessau bisa zarginsu da kasancewa ummal’aba’isin wani bakar fata dan kasar Saliyo, wanda ya kone kurmus lokacin da yake tsare a gidan wakafi. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta yi bitar matsalar tana mai cewar:

“A daidai ranar bakwai ga watan janairun shekara ta 2005 a wajejen karfe 12 na rana ne Ouri Jallo ya rasu. Kuma a lokacin mutuwar tasa an daure hannuwansa da kafafuwansa da katifa. Bincike kuma ya tabbatar da cewar konewa yayi kurmus. To sai dai kuma akwai tababa a game da ikirarin da ake yi na cewar ‘yan sanda ba su mayar da martani akan lokaci ba bayan da kararrawa da rika kadawa domin gangami a game da yiwuwar samuwar gobara a daya daga cikin dakunan gidan wakafin. Kungiyoyin kare hakkin dan-Adam na tattare da imanin cewar wani kokari ake yi a yi rufa-rufa da ainifin abin da ya faru, musamman idan an ba da la’akari da jinkirin da aka yi wajen gabatar da shari’ar. Domin kuwa an san ‘yan sandan jihar Sachsen-Anhalt dake gabacin Jamus da muzanta wa baki. A saboda haka wannan bayanin na tattare da walakin.”

A wannan makon ministocin raya kasashe masu tasowa na gamayyar G8 dake da ci gaban masana’antu suka gudanar da taronsu a birnin Berlin domin nazarin hanyoyin bunkasa al’amuran zuba jari a kasashen Afurka. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG tayi sharhi tana mai cewar:

“A shekarun baya-bayan nan da yawa daga kasashen Afurka na samun bunkasar sama da kashi biyar cikin dari ga tattalin arzikinsu sakamakon kwararan matakai da suke dauka na garambawul, a sakamakon haka ne Jamus, dake shugabancin gamayyar G8 a halin yanzu ta tsayar da shawarar mara wa wannan ci gaba da ake samu ta yadda zai zama mai dorewa.”