Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 10.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Zaben Nijeriya na ci gaba da shiga kannon rahotannin jaridun Jamus

Shugaba Mugabe

Shugaba Mugabe

Azabtar da ‘yan gudun hijirar Somalia a sansanonin gwale-gwale a kasar Habasha, hali da ake ciki a kasar Zimbabwe da kuma bude kofofin kasuwannin kasashen KTT ga kasashen gamayyar ACP na Afurka da Karibiya da kuma Pacific, wadannan su ne muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin da jaridun Jamus suka gabatar dangane da nahiyar Afurka a wannan makon mai karewa..Amma da farko zamu fara ne da duba wani dogon rahoton da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta dangane da zaben Nijeriya, inda take cewar:

“Ba tare da tsoron Allah ba shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ke daukar matakai na nadin mutumn da yake son ganin ya gaje shi. A halin yanzu haka kasar Nijeriya na kan hanyar fuskantar mummunar kalubala, wadda aka dade ana tsoron afukuwarta bayan da kotun koli ta tarayya ta ki amincewa da tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. Shi dai Atiku yana daya daga cikin ‘yan takarar da ake kyautata zaton zasu taka muhimmiyar rawa a zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga wannan wata, amma hukumar zabe ta kasa ta sa kafa tayi fatali da ‘yancinsa na tsayawa takarar zaben bisa zarginsa da laifuka na cin hanci sakamakon takun sakar dake akwai tsakaninsa da ainifin tsofon amininsa shugaba Olusegun Obasanjo.” Jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce wannan take-taken na Obasanjo na mai yin nuni ne da bakin kokarinsa da yake yi na ganin zaben ya haifar da sakamakon da ya dace da bukatunsa.

Rahotanni masu nasaba da kungiyoyin kare hakkin dan-Adam sun ce an tasa keyar ‘yan gudun hijirar Somaliya daga sansanoninsu dake kasar Kenya domin tsare su a sansanonin gwale-gwale a kasar Habasha. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

“Rahotanni masu nasaba da kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Human Right Watch dake birnin New York sun ce a cikin watan janairu kadai an kame ‘yan gudun hijirar Somaliya sama da 100 a kasar Kenya abin da ya hada har da yara kanana kuma aka kwashe su a cikin dare aka kai su Mogadishu aka danka su hannun sojojin mamaye na kasar Habasha. Su kuma a nasu bangaren suka tasa keyarsu zuwa Habasha, inda aka tsaresu domin fuskantar tambayoyi daga jami’an leken asiri na Amurka. Wasu rahotannin ma sun ce ba kawai ‘yan kasar Somaliya din ne ake kamewa a asurce domin kai su Habasha ba, har da sauran ‘yan kasashen ketare kamar wata da ake kira Kamiliya Muhammed daga hadaddiyar daular kasashen Larabawa, wadda aka kame a farkon watan janairun da ya gabata duk da cewar bata da wata alaka da kasar Somaliya. Akwai kuma cikakkun rahotanni na hukumar leken asirin Amurka ta CIA da ta ‘yan sandan ciki ta FBI dake tabbatar da haka.”

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung lekawa tayi kasar Zimbabwe ta kuma nuna cewar daya daga cikin dalilan da suka sanya shugaba Robert Mugabe ke cin karensa babu babbaka shi ne goyan baya da yake da shi tsakanin kasashen kudancin Afurka a matsayin jigon fafutukar neman ‘yancin kai, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samarwa da kasar Zimbabwe ‘yancin kanta. Bugu da kari kuma shi kansa shugaban ATK Thabo Mbeki sai da yayi tofin Allah tsine akan masu neman ganin an kakaba wa Zimbabwen takunkumin karya tattalin arziki, ya ce masu irin wannan kira suna nesa ne da ainifin matsalar da ake fama da ita.

A wani ci gaban da aka samu KTT ta tsayar da shawarar yi wa kasashen ACP sassaucin ciniki tun abin da ya kama daga shekara ta 2008. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi bitar lamarin tana mai cewar:

“Kasashe 77 na gamayyar ACP zasu samu cikakkiyar damar shigo da dukkan kayayyakin da suke sarrafawa abin da ya hada har da amfanin noma zuwa kasashen kungiyar ba tare da kayyade musu kaso ko biyan kwasta ba tun daga shekara ta 2006. To sai dai kuma kungiyar ciniki ta duniya bata gamsu da wannan shawara da ta fito daga bangare daya ba kuma a saboda haka a nasu bangaren kasashen na ACP su ma zasu bude kasuwanninsu sannu a hankali ga kayayyakin kasashen Turai.”