1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

July 6, 2007

Taron kolin shuagabannin AU shi ne ya dauki hankalin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPE

Zamu fara ne da taron kolin shuagabannin kasashen kungiyar tarayyar Afurka AU, da aka gudanar a wannan makon a birnin Accra na kasar ghana, domin shi ne muhimmin abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus akan al’amuran Afurka a wannan makon. A cikin nata sharhin dai jaridar Süddeutsche Zeitung ta bayyyana ra’ayinta ne kamar haka, inda take cewar:

“Taron kolin kungiyar tarayyar Afurka ya kawo karshensa tare da mummunan kaye ga shugaban Libiya Mu’ammar Gaddafi. Bayan shawarwari na tsawoin yini uku a Accra fadar mulkin kasar Ghana shuagabannin kasashe sama da 50 sun bayyana rashin goyan bayansu ga shawarar kafa wata gwamnati bai daya ta kasashen Afurka nan take.”

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

“Taron kolin shuagabannin kasashen kungiyar tarayyar Afurka ya zo karshensa tattare da rudami. Wannan maganar kuwa ta shafi shawarar shugabab Libiya ne wanda ke bukatar ganin an kafa wata gwamnati ta hadaddiyar daular Afurka. Ko da yake shugaban na Libiya na samun goyan baya daga takwaransa na Senegal Abdoulaye Wade, amma sauran shuagabannin Afurkan basa tattare da wannan ra’ayi, inda suke ba da fifiko ga karfafa matsayin kungiyoyin hada-ka na yankuna.”

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

“Abin takaici game da taron kolin shuagabannin kungiyar tarayyar Afurka a birnin Accra shi ne kasancewar ba a ba da la’akari sosai yadda ya kamata ba da matsalolin dake addabar nahiyar Afurka, kamar rikicin Darfur da Somaliya da Kongo da kuma Cote d’Ivoire. Domin wadannan rikice-rikice wajibi ne a nemi bakin zaren warwaresu, amma a maimakon haka sai aka shiga sabani akan shawarar Gaddafi game da kafa wata hadaddiyar daular kasashen Afurka.”

Dangane da rikicin Darfur jaridar Die Welt ta duba halin da ‘yan gudun hijirar yankin suke ciki inda take cewar:

“’Yan gudun hijirar Darfur, ko da sun tsallake zuwa kasar Chadi ba su tsira ba. Domin kuwa dakarun Janjawid na larabawa su kan kutsa wasu kauyuka na kan iyakar Chadin domin kai musu farmaki. Bugu da kari kuma akwai rahotannin dake nuna muzantawar da su kan sha fama da ita daga bangaren sojojin kasar ta Chadi. Wato dai a takaice ‘yan gudun hijirar sun gudu ne amma ba su tsira ba.”

A wannan makon ma dai maganar kamfanin sarrafa maganin nan na Amurka Pfizer ya sake daukar hankalin masharhanta na Jamus, inda jaridar Die Tageszeitun take cewar:

“A sakamakon tabargazar da kamfanin Pfizer ta caba wajen gwaje-gwajen wasu magunguna akan yara kanana da wasu majiyata, wadanda daga baya ko dai sun halaka ko kuma sun samu nakasa tsawon rayuwarsu, dubban dubatar mutane a arewacin Nijeriya suka ki yarda da ayi wa ‘ya’yansu lambar riga kafin shan inna. An ma samu masu yada farfagandar cewar ainifin magungunan riga kafin ba kome ba ne illa kawai magungunan da ake nema da a yi amfani da su domin hana matan musulmi hayayyafa. Ba kowa ba ne ummal’aba’isin wannan mummunan ci gaba face kamfanin Pfizer.”