Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 13.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Maganar Zimbabwe ce ta fi daukar hankalin masharhanta na Jaridun Jamus a wannan mako

'Yan zanga-zanga a Zimbabwe

'Yan zanga-zanga a Zimbabwe

A wannan makon mawuyacin hali na rayuwa da al’umar Zimbabwe ke ciki shi ne babban abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon. Amma da farko zamu fara ne da wani rahoto da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta a game da yadda bankin duniya ke yabawa da ci gaban da kasashen Afurka masu bin tafarkin demokradiyya ke samu ga tattalin arzikinsu. Jaridar ta ce:

“Rahoton da bankin duniya ya bayar ya yaba wa irin ci gaban da kasashen Afurka suka samu, musamman ma ‘yan rabbana ka wadata mu daga cikinsu, wadanda suka samu ci gaba a cikin dan gajeren lokaci. Daga cikin kasashen Afurka da suka samu ci gaba kuwa har da Kongo da Ruwanda da Nijer da Liberiya da kuma Tanzaniya. Amma a daya bangaren kuma akwai kasashen da suka fuskanci koma baya, wadanda suka hada da Zimbabwe da kuma Cote d’Ivoire.”

Kasar Zimbabwe dai kamar yadda muka yi bayani tun farko ita ce tafi daukar hankalin jaridun na Jamus a wannan makon sakamakon mawuyacin hali na rayuwa da al’umarta ke ciki. Jaridar Berliner Zeitung ta yi bitar lamarin tana mai cewar:

“Kasar Zimbabwe na dada durmuya a cikin mawuyacin hali na tattalin arziki, inda aka samu hauhawar farashin kaya da misalin ninki uku a cikin mako daya kacal. Tun dai abin da ya kama daga shekara ta 2000 kawo yanzu kasar tayi asarar kashi 50% na angizon tattalin arzikinta kuma a halin da ake ciki yanzu haka tafi fama da kaka-nika-yi akan duk wata kasar da yakin basasa yayi kaca-kaca da ita a doron duniyar nan tamu.”

Ita ma jaridar kasuwanci ta Handelsblatt ta yi nazarin wannan mawuyacin halin da Zimbabwe ke ciki, inda take cewar tattalin arzikin kasar na dab da wargajewa kwata-kwata. Jaridar ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

“A dai halin da ake ciki yanzun ana fama da rashin kayan masarufi na yau da kullum a yankunan karkara kuma nan ba da dadewa ba wannan bala’i zai rutsa da birane, muddin gwamnati ba ta canza salon kamun ludayinta a game da manufofin farashin kaya ba. Domin tinkarar matsalar hauhawar farashin kaya na sama da kashi dubu hudu cikin dari shugaba Mugabe ya ba wa ‘yan kasuwa umarnin rage farashin kayayyakinsu fiye da kashi 50%. Amma kuma ‘yan tireda ba zasu iya sayar da kayayyakin nasu kasa da abin da suka sara ba da farko ba. Muddin ana fatan shawo kan matsalar tilas ne matakin na gwamnati ya hada da kowa da kowa kama daga masu sarrafa kayayyakin da masu shigowa dasu daga ketare da kuma masu sararsu a kasar ta Zimbabwe.”

A sakamakon dimbim arzikin mai da Allah Ya fuwace wa nahiyar Afurka, a halin yanzu Amurka na bakin kokarinta wajen tabbatar da angizonta a wannan nahiya, a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung lokacin da take ba da rahoto akan shirin kasar ta Amurka na kafa sansanin sojanta a Afurka. Jaridar ta ce ko da yake Amurka na ikirarin daukar matakai ne na murkushe ayyukan ta’adda amma a hakikanin gaskiya arzikin mai da Allah Ya fuwace wa Afurka kama daga arewacin nahiyar zuwa kudancinta da kuma yammaci tun daga makurdadar Guinea zuwa Nijeriya da Sao Tome da Principe, shi ne ainihin dalilin da ya sanya Amurka ke kara kutsa kai a wannan nahiya.

Mujallar Der Spiegel a nata bangaren ta bayyana mamakinta ne a game da yadda duniya ke wa rikice-rikicen nahiyar Afurka rikon sakainar kashi inda ta lissafta yankuna daban-daban da ake fama da rikici a cikinsu kama daga Somaliya zuwa Sudan da Chadi da janhuriyar Afurka ta Tsakiya, wadda mujallar ta ce ba kasafai ba ne ma ake jin duriyarta.