Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 20.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

A wannan makon ma maganar Zimbabwe ta sake shiga kanun rahotannin jaridun Jamus

A wannan makon dai daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan al’amuran Afurka har da shawarar kungiyar tarayyar Turai a game da tsugunar da sojojin tsaron zaman lafiya na kungiyar a kasar Chadi. Amma da farko zamu fara ne da duba kasar Somaliya, inda a wannan makon aka sake gabatar da wani sabon taron sulhu a kokarin shawo kan rikicin kasar da ya ki ci ya ki cinyewa. Sai kuwa da aka rika dage taron sakamakon rigingimun da aka yi ta fuskanta a Mogadishu fadar mulkin kasar ta Somaliya. A lokacin da take gabatar da rahoto akan haka jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

„Mutane da dama musamman kungiyoyin taimako masu zaman kansu sun nuna rashin kwarin guiwarsu a game da wannan taro saboda ba a gayyaci wakilan kasar Eritrea ba, wadda ake kyautata zaton cewar ita ce ke goya wa masu zazzafan ra’ayi na musulunci baya. Kasar Habasha, ita ce ta taimaka aka fatattaki kungiyoyin musulmin daga fadar mulki ta Mogadishu kuma tun daga sannan kungiyoyin suka koma sunkuru suna masu jefa mazauna birnin cikin hali na rudu da rashin sanin tabbas. Bugu da kari kuma da yawa daga ‚yan Somaliya na kyamar sojojin mamaye na Habasha, wadanda wanzuwarsu a kasar ka iya hana ruwa gudu wajen samun nasarar taron na sulhu.“

Har yau ana ci gaba da fama da tabargazar nan ta smoga da ake zargin jami’an MDD da cabawa a kasar Kongo, inda aka ce suna da hannu dumu-dumu wajen fitar da wasu ma’adinai daga kasar ba a bisa ka’ida ba. Jaridar Die Tageszeitung tayi bitar lamarin tana mai cewar:

„Wannan zargin ya jibanci wani yanki ne da ake kira Nyabiondo dake da tazarar kilomita 80 daga Goma, shelkwatar arewacin lardin Kivu, inda wasu daidaikun dakarun sa kai ke da angizo. An ce sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD daga kasar Indiya kann yi musayar kayan masarufi a madadin gwal tare da dakarun kungiyar tawaye ta FDLR. Ita wannan kungiyar ce kuwa ke hana ruwa gudu wajen cimma zaman lafiyar Kongo. Sau tari mutane a wannan yankin sun sha mamakin ganin yadda dakarun kungiyar kann samu ikon janyewa akan lokaci bayan sun kai hare-harensu na sunkuru. A halin yanzu haka kungiyar ce ke da hannu akan rijiyoyin hakan gwal a Nyabiondo, tana mai murkushe dukkan martanin da sojoji da kuma dakarun hadin guiwa na ‚yan tawayen Tutsi da na Kongo ke mayarwa.“

Sabon shugaban kasar Faransa Nikolas Sarkozy, kamar yadda manazarta suka lura, yana fama da lalube ne a cikin dufu a manufofinsa dangane da kasashen Afurka, inda a wannan makon ya gayyaci shugaba Idriss Deby domin tattaunawa a game da tsugunar da sojojin Faransar a Chadi a daura da shawarar da Sarkozy ya bayar ta tsugunar da sojojin kiyaye zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Turai a Chadin domin taimakawa wajen kyautata tsaro da ba da kariya ga ayyukan taimakon jinkai a Darfur. To sai dai kuma kamar yadda jaridar frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito tuni Jamus ta ce ba ta ba shigar da sojojinta a irin wannan runduna ta kwantar da tarzoma, musamman ma ganin cewar babu wata takamaimiyar yarjejeniya ta zaman lafiyar da aka cimma a wannan yanki.

Kasar Zimbabwe na dada kutsawa cikin mawuyacin hali na kaka-nika yi. Jaridar Neues Deutschland ta sake bitar wannan mawuyacin hali inda take cewar:

„A samamakon mawuyacin hali na rayuwa inda ake samun hauhawar farashin kaya ta sama da kashi 4500 cikin dari al’umar Zimbabwe ke juya wa kasarsu baya. A halin yanzu haka sama da kashi kimanin kashi daya bisa uku na al’umar kasar sun dogara ne kacokam akan taimakon abinci daga ketare. Bugu da kari kuma tsarin kiwon lafiya ya tabarbare kwata-kwata. Ga rashin wutar lantarki. Kawo yanzu sama da ‚yan kasar Zimbabwe miliyan hudu suka yi kaura zuwa ketare, kama daga likitoci da injiniyoyi da sauran kwararrun ma’aikata. Lamarin ya zama kamar dai abin da Hausawa ke cewa ne wai iya ruwa fid da kai. Duk wani mai iko sai ya tattara nasa ya nasa ya san inda dare yayi masa.“