1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

August 3, 2007

Kudurin MDD akan lardin Darfur shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan mako

https://p.dw.com/p/BvPB
sojan kiyaye zaman lafiya a Darfur
sojan kiyaye zaman lafiya a DarfurHoto: AP

A wannan makon dai kudurin MDD akan kasar Sudan shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus dangane da al’amuran nahiyarmu ta Afurka. Amma da farko zamu fara ne da wani rahoton da jaridar Kölner Stadt-Anzeiger ta rubuta inda tayi bitar ci gaban da aka samu a kasar Kongo shekara daya bayan zaben kasar da aka gudanar. Jaridar ta ce:

„Har yau dai kasar bata fara farfadowa daga tabarbarewar tattalin arzikinta ba. Kazalika tana fama da rashin hanyoyin sadarwa, wadanda yakin basasa da mulkin kama karya suka yi kaca-kaca da su. Akasarin al’umar kasar suna zama ne hannu baka hannu kwarya duk da dimbin arzikin da Allah ya fuwace mata hade da kasar noma mai albarka. Kasar har yau bata da zaman lafiya, kuma sojoji da dakarun sa kai sun mayar da fyade ga mata tamkar wani muhimmin makami a rikicin kasar da aka ce kasar Ruwanda ce ke kara rura wutarsa.”

A wani kyakkyawan ci gaba da aka samu kuma a wannan makon aka yi bikin kone makamai a garin Bouake tare da halarcin shugaba Laurent Gbagbo da madugun ‘yan tawaye Guillaume Soro domin zama wata shaida ta sake hadewar kasar Cote d’Ivoire bayan rarrabuwa ta tsawon shekaru biyar sakamakon yakin basasa. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

„A hakika dai ba tabbas ko kasar ta Cote d’Ivoire a yanzun zata samu zaman lafiya mai dorewa. Domin kuwa kusan wata daya da ya wuce P/M Guillaume Soro ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kisan gillar da aka yi masa, kuma manazarta na tattare da imanin cewar mukarraban Soro din ne ke da alhakin wannan yunkurin da ya wakana a Bouake. Bugu da kari kuma wasu daga cikin ‚yan tawayen zasu fi kaunar ci gaba da yakar Gbagbo a maimakon sulhu a cikin ruwan sanyi saboda akidarsa ta kabilanci da wariyar addini. Makomar zaman lafiyar dai ta danganta ne da irin rawar da Gbagbo da Soro zasu taka wajen kwance damarar masu tsattsauran ra’ayi tsakanin magoya bayansu.“

A wani ci gaban kuma a wannan makon MDD ta tsayar da kudurin tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa lardin Darfur na kasar Sudan. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

„Ba za a iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lardin Darfur da karfin hatsi ba, muhimmin abu shi ne a sake farfado da shawarwarin zaman lafiya tsakanin sassan da rikicin lardin ya shafa. Kuma ko da yake fadar mulki ta Khartoum ta bayyana gamsuwarta da kudurin na MDD, amma fa an dade ana famar kai ruwa rana tare da ita a game da shigar da sojan MDD a matakn kiyaye zaman lafiya a kasar, kuma mai yiwuwa a wannan karon ma daga baya ta tubre.“

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a cikin nata sharhin cewa tayi:

„Tuni murna ta koma ciki game da ainifin manufar MDD dangane da lardin Darfur, inda a shekara ta 2005 lokacin wani taron kolin kasa da kasa a birnin New York aka yi batu game da alhakin dake akwai na ba da kariya ga jama’a. Wannan maganar ta shafi katsalandan ko ta halin-kaka domin kare lafiyar jama’ar kasa idan gwamnati ta gaza. Amma sojan kiyaye zaman lafiya na MDDr ba su da irin wannan damara sannan su kuma kasashen majalisar ba su goyan bayan hakan a siyasance. A saboda haka mutane zasu ci gaba da fama da kaka-nika-yi game da makomarsu wadda ta ta’allaka da bukatun masu cin zarafinsu ko kuma maslahar kasar China, kamar yadda lamarin yake a zahiri dangane da lardin Darfur.“