1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

August 24, 2007

Bikin ranar cinikin bayi na daga cikin muhimman batutuwan da jaridun Jamus suka duba a wannan makon

https://p.dw.com/p/BvP9

Daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin Jamus akan al’amuran nahiyarmu ta Afurka a wannan makon har da bikin ranar bayin da aka gudanar a wajejen tsakiyar mako. Amma da farko zamu fara ne da duba halin da ake ciki a kasar Somaliya, inda jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta sharhi tana mai korafi akan abin da ta kira gazawa a Somaliya. Jaridar ta ce:

“Kwamitin sulhu na MDD ya sake bayyana yadda yake wa matsalar kasar Somaliya rikon sakainar kashi. Domin kuwa ko da yake ya amince da wani kudurin tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Somaliyar ba tare da musu ba, amma babu wani takamaiman bayanin da aka yi a wannan kudurin a game da sojojin da za a tura. An dangana alhakin lamarin ne kacokam akan kasashen Afurka, wanda hakan babban kuskure ne kuma abin kunya ga MDD. Idna har ita kanta MDD na jin tsoron tura sojojinta zuwa Somaliya, ta yaya zata sa ran cewar wasu sojoji ‘yan kalilan daga Uganda zasu iya magance lamarin.”

A kasar Sudan an fara fuskantar matsala dangane da makomar yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da kungiyar SPLM a kudancin kasar sakamakon rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a Darfur. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ce ta fadi hakan ta kuma kara da cewar:

“Duk wanda ya duba dubbannin sojojin kiyaye zaman lafiya da aka tanadarwa da kasar Sudan, wadanda yawansu ya kai dakaru dubu 36, zai yi zaton cewar nan ba da dadewa ba zaman lafiyar kasar zai tabbata, amma fa lamarin ba haka yake ba. Domin kuwa a daidai lokacin da kafofi na kasa da kasa suka dukufa wajen samar da zaman lafiya a yammacin makekiyar kasar ta Afurka, a daya bangaren ana fuskantar barazanar wargajewar tsarin zaman lafiya sannu a hankali a kudancinta sakamakon watsin da aka yi da wannan yanki. Shugaba al-Bashir da jam’iyyarsa ta NCP na kiyawa kememe da manufar raba madafun mulki tare da tsofuwar kungiyar tawaye ta SPLM, kamar yadda yarjejeniyar zaman lafiyarsu da aka cimma a shjekara ta 2005 ta tanada domin kawo karshen yakin basasar kasar ta Sudan na tsawon shekaru 21.”

Bisa ga dukkan alamu dai murna ta koma ciki a game da niyyar kasar Chadi ta nuna wa bankin duniya cewar al’umar kasar zasu amfana daga arzikin man fetir da Allah Ya fuwace mata. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

“A shekara ta 2003 ne aka fara hakan mai a kasar Chadi, kuma a saboda kasancewar jami’an siyasar kasashen Afurka dake da arzikin mai sun shahara da wawason dukiya da almubazzaranci da ribar da ake samu daga wannan arziki bankin duniya yayi hadin kai da shugaba Idris Deby domin tsara wata dokar da zata taimaka al’umar kasa su amfana daga wannan arziki. Amma fa abin takaici a nan shi ne kasancewar shekaru hudu bayan fara hakan man fetir din har yau kasar Chadi ce cikon ta bakwai a cikin jerin kasashe ‘yan rabbana ka wadata mu dake fama da mummunan talauci a duniya.”

A wajejen tsakiyar mako ne aka tsayar da bikin ranar bayi ta duniya, inda jaridar Neues Deutschland tayi amfani da wannan dama domin waiwayar baya da kuma bitar halin da ake ciki a game da wannan mummunan matsala da ta zama kazamin tabo ga tarihin dan-Adam. Jaridar ta ce:

“A tsakanin shekara ta 1550 zuwa shekara ta 1850 an sayar da bakar fatar Afurka sama da miliyan 50 domin aikin bauta a Amurka da Turai da sauran sassa na duniya, kuma sai tare da gwagwarmaya iri daban-daban da sadaukar da rayuka aka kai ga haramta wannan danyyen ciniki akalla a rubuce. Domin kuwa har yanzu cinikin bayin na ci gaba da wanzuwa sakamakon kusantar junan da ake dada samu tsakanin sassan duniya domin zama karkashin rumfa daya. An kiyasce cewar yara kimanin miliyan 250 dake da shekaru tsakanin biyar da 14 na haifuwa suke aiki na bauta a sassa daban-daban na duniya yanzu haka.”