Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 21.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Ambaliyar ruwa a nahiyar Afurka ita ce ta mamaye kanun rahotannin jaridun Jamus akan nahiyar

Babban abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a game da al’amuran Afurka a wannan makon mai karewa shi ne ambaliyar ruwa mai tsananin gaske da ta rutsa da yankin Sahel na nahiyar Afurka, kama daga yammaci zuwa gabacin nahiyar. Amma da farko zamu fara ne da duba wani ci gaban da aka samu a kasar Zimbabwe a wannan makon inda majalisar dokokin kasar ta amince da gudanar da tagwayen zabubbuka na majalisar dokoki da shugaban kasa watan maris shekara mai zuwa. ‘Yan hamayya sun ba da goyan baya wajen cimma wannan manufa madaidaiciya da zata kawo canji ga daftarin tsarin mulkin kasar Zimbabwe, abin da ya hada har da bai wa majalisar dokokin damar zaben wanda zai gaji shugaba Mugabe kai tsaye idan har ya amince da yayi murabus gaba da wa’adi. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung ta ce mai yiwuwa wannan canjin ya zama wani kyakkyawan ci gaba akan hanyar gudanar da zabe akan wata turba ta demokradiyya da adalci a wannan kasa shekara mai zuwa.

Kasashen Afurka na fama da wata mummunar Ambaliya, wadda nahiyar ba ta taba ganin irin shigenta ba a cikin shekaru darin da suka wuce. Domin kuwa ambaliyar ta fara ne tun daga yammaci ya zuwa gabacin nahiyar, kuma akalla tayi sanadiyyar rayukan mutane 270 a baya ga dubban daruruwan da suka yi asarar gidajensu. A lokacin da take bitar wannan matsala jaridar Neues Deutschalnd cewa tayi:

“Damina da ta saba kawo wa kasashen Afurka albarka, bana ta rikide ta zama masifa gare su. Hatta kasashe irinsu Mali da Niger da Sudan, wadanda ke da yanayi na fari, bana ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka rika yi a makonnin baya-bayan nan ya kai musu iya wuya. Ambaliyar da zama gama gari tun abin da ya kama daga Senegal zuwa Burkina Faso da Nigeria da Chad a yammaci da Habasha da Uganda da Kenya a gabacin Afurka. An kiyasce cewar mutane sama da miliyan daya da rabi ke fama da radadin wannan bala’in a yankunan da ya shafa.”

Ita ma jaridar Frankfurter Rundschau tayi bitar ambaliyar da ta ce ta rutsa da kasashe ashirin a nahiyar Afurka. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Ruwa da tabo na mamayar yankunan nahiyar Afurka, kama daga Habasha a gabaci zuwa Mauritaniya a yammacin nahiyar. A halin da ake ciki yanzun tuni MDD ta kada gangami, inda ta ce a kasashe 18 daga cikin kasashe 20 da bala’in ambaliyar ya shafa akwai barazanar billar cututtuka sakamakon gurbacewar ruwan sha. Wasu rahotannin ma sun ce tuni cutar gudawa ta kolera ta billa a kasashen Ghana da Sudan. A baya ga haka ana sa ran fuskantar farin dango dake lalata amfanin noma, kamar yadda aka saba gani a lokuta na damina.”

A kasar Saliyo an samu canjin gwamnati sakamakon nasarar da mataimakin shugaban kasa Ernest Bai Koroma na jam’iyyar APC ya samu a zaben raba gardamar da aka gudanar inda ya tashi da rinjayen kashi 54 da rara cikin dari. Jaridar Süddeutsche Zeitung ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“A yakinsu na neman zabe, dukkan jam’iyyun siyasar saliyo sun yi wa jama’a alkawarin ta da komadar tattalin arzikin kasar da yakar cin hanci da almubazzaranci. Ga alamu kuwa al’umar kasar sun fi sikankancewa ne cewar jam’iyyar APC ce zata iya biya musu wannan bukata, saboda ita SLPP ta sha fama da tabargazar cin hanci a baya-bayan nan, lamarin da ya sanya suka manta da tabargazar ita APC, wadda kafin yakin basasar kasar ta mayar da Saliyo karkashin tsarin mulkin jam’iyya daya tare da muzanta wa ‘yan hamayya. A takaice dai wannan zaben ya bayyanar ne a fili cewar al’umar Saliyo na sha’awar rungumar demokradiyya da hannu biyu-biyu.”