Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 28.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana goyan bayansa ga shawarar tura sojan KTT zuwa Cadi

A wannan makon, ko da yake mawuyacin halin da ake ciki a Myanmar da kuma taron babbar mashawartar MDD da ake gudanarwa a birnin New York su ne suka fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, amma a daya bangaremn jaridun sun yi amfani da taron asusun taimako na kasa da kasa a birnin Berlin domin bitar halin da kasashen Afurka ke ciki. A cikin nata rahoton dai jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

“An kammala taron kasashen dake ba da lamuni ga asusun taimako na kasa da kasa a birnin Berlin tare da alkawururrukan taimakon kudade masu tarin yawa domin yaki da cuttukan Aids da zazzabin cizon sauro da tarin fuka. Gaba daya an yi alkawarin ba da taimakon jumullar kudi na dala miliyan dubu tara da dari bakwai tsakanin shekara ta 2008 zuwa ta 2010. To sai dai kuma ko da yake tsofon sakatare-janar na MDD Kofi Annan ya ce wadannan kudaden zasu taimaka wajen ceton rayukan mutane masu tarin yawa, amma an yi tsokaci da cewar ko da an cika wadannan alkawururruka kudin ba zasu isa ba, domin kuwa abin da ake bukata ya kai dala miliyan dubu 12 a tsakanin wadannan shekaru guda uku, ita kuma kafar MDD mai yakar Aids ta ce ainifin abin da ake bukata zai kai dala miliyan dubu 42 domin jiyyar masu fama da cutar a duk fadin duniya a tsakanin wadannan shekaru uku.”

Ita kuwa jaridar Freitag ta sake bitar mawuyacin halin da kasashen Afurka suka sake samun kansu a cikin ne sakamakon ambaliyar ruwan nan da ta rutsa da yankin sahel kama daga yammaci zuwa gabacin Afurka, inda ta ce bayan fari sai dufana. Jarida ta kara da cewar:

“Mutane sama da miliyan daya da rabi ke bukatar taimakon abinci a cikin gaggawa a yayinda aka ce wasu dubu 600 kuma sun rasa gidajensu a baya ga wasu 250 da suka mutu. Dukkan wadannan alkaluma kiyasi ne aka bayar amma ba wanda ya san tahakikanin yawan mutanen dake fama da hali na zautuwa sakamakon wannan bala’in da kuma cututtuka irinsu kwalera da zazzabin cizon sauron da ake fargabar zasu biyo baya.”

Dangane da yaki da zazzabin cizon sauro, a shekarar da ta wuce kungiyar lafiya ta duniya WHO ta bayyana niyyarta ta ba da shawara da aiwatar da maganin kashwe kwarin nan na DDT da aka haramta amfani da shi a Jamus da Amurka sakamakon illar da yake haifarwa ga lafiyar dan-Adam. Hujjar kungiyar game da shawarar ita ce wai nasarar da aka samu wajen kayyade yaduwar cutar sakamakon aiwatar da maganin na DDT a yankin Kwazulu na ATK. Jaridar Der Tagesspiegel tayi bitar lamarin tana mai cewar:

“A hakika ana iya tinkarar zazzabin cizon sauro ba tare da aiwatar da maganin kashe kwari na DDT ba, kamar yadda aka gani a kasar Mexiko, wadda ta haramta DDT a 2000 ta kuma mayar da hankalinta akan matakai na tsafta, wadanda kuma ba su da lahani ga makomar kewayen dan-Adam.”

A wannan makon kwamitin sulhu na MDD ya yanke shawara a game da tura sojan kiyaye zaman lafiya na KTT zuwa Chadi, amma a daya bangaren kamar yadda jaridar Die Tageszeitung take gani, su kansu kasashen kungiyar ba su da cikakkiyar niyyar yin katsalandan, jaridar ta ci gaba da cewa:

“Ko da yake a karo na farko shugaban Amurka ya fito fili yana mai batu a game da kisan kiyashi a Darfur, amma fa sai da aka sha fama da kai ruwa rana a game da wanzuwar sojojin Faransa a nahiyar Afurka a mahawarar ta kwamitin sulhu, kuma tuni ‘yan tawayen kasar Chadi suka yi barazanar kai farmaki kan sojojin kiyaye zaman lafiyar na KTT, muddin sun ga wata alamar dake nuna cewar sojojin za a tsugunar da su ne domin su rufa wa mayakan kasar Faransa dake kasar ta Chadi baya.”