1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

October 12, 2007

Dubban miliyoyin kudaden taimako da ake aiwatarwa a yake-yaken basasar Afurka shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta

https://p.dw.com/p/BvP4

Muhimmin abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon shi ne wani rahoton dake bayani akan makudan kudin da kasashen Afurka ke asararsu a kowace shekara sakamakon yake-yake na basasa. Kungiyoyin taimako na kasa da kasa da suka hada da Oxfam da Safeworld da kuma Iansa suka gabatar. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“Ta la’akari da dubban miliyoyin kudaden da kasashen Afurka ke asararsu sakamakon yake-yake na basasa, inda alkaluma suka nuna cewar gaba daya kasashen da lamarin ya shafa sun kashe abin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu dari biyu da tamanin da hudu tsakanin 1990 zuwa shekara ta 2005, ya zama wajibi a albarkaci yarjejeniyar nan ta haramta cinikin kananan makamai a cikin gaggawa.”

Ita kuwa jaridar Die Welt a cikin nata rahoton tayi nuni ne da yadda yake-yake na basasa ke handume kudaden taimakon raya kasa, a kasashen Afurka 23 da aka yi bincike kansu. Amma jaridar sai ta kara da cewar:

“Wadannan alkaluman da aka bayar ba su hada da kudaden da aka kashe wajen sayen makamai a lokuta na zaman lafiya ba ko kuma kudaden da ake kashewa a ayyuka na kiyaye zaman lafiya da taimakon jinkai da tasirin ‘yan ta-kife. Domin kuwa aikin kiyaye zaman lafiya na MDD a kasar Kongo ya kan ci abin da yayi sama da dalar Amurka miliyan dubu daya a shekara, ga kuma tasirin da ire-iren wadannan tashe-tashen hankula ke yi akan tattalin arzikin kasashe makobta.”

Kasar ta Kongo dai har yau babu wata alamar dake nuna cewar zata samu zaman lafiya da kwanciyar hankali nan ba da dadewa ba duk da wadannan makudan kudin da ake kashewa kanta, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito ta kuma kara da cewar:

“A halin yanzu yakin basasar kasar Kongo ya dauki wani sabon fasali na kabilanci, inda Nkunda ke da goyan bayan kabilar Hutu dake fafatawa da ‘yan tawayen Tutsi.”

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a wannan makon lekawa tayi kasar Sudan inda tayi korafin cewar sojojin kasar sune ke rura wutar yakin basasar Darfur. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Babbar shaida game da haka ita ce harin da sojojin suka kai kan garin Haskanita, inda suka aske garin kwata-kwata sai kawai wata makaranta daya da wani masallaci suka baro a baya. Ko da yake sojojin na neman dora wa ‘yan tawaye alhakin wannan ta’asa, amma fa su ‘yan tawayen ba su da tankoki ballantana jirgaen saman yaki.”

Ko da yake kasar Mali na daya daga cikin kasashe ‘yan rabbana ka wadata mu a duniya, amma tuni ta zama abin koyi ga sauran kasashen Afurka, kamar yadda jaridar Die Zeit ta nunar ta kuma kara da cewar:

“Kasar Mali na da dukkan kafofin da ake bukata domin tafiyar da mulki na demokradiyya tsantsa. Kasar na da hukumar zabe mai zaman kanta da jam’iyyun siyasa masu tarin yawa da majalisar dokoki tana kuma bakin kokarinta wajen yaki da cin hanci tun abin da ya kama daga matsayi na kananan hukumomi zuwa ga matsayi na gwamnati, kuma wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanya kasar take samun taimakon raya kasa, amma ba saboda kasancewarta ‘yar rabbana ka wadata mu ba.”