Afurka A Jaridun Jamus | Siyasa | DW | 13.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afurka A Jaridun Jamus

Har yau halin da ake ciki a Somaliya na ci gaba da daukar hankalin jaridun Jamus

'Yan gudun hijirar Somaliya

'Yan gudun hijirar Somaliya

Hali da ake ciki a Mogadishu, fadar mulkin kasar Somaliya, matsin kaimi da MDD da Kungiyar tarayyar Afurka ke wa gwamnatin Sudan da kara tabarbarewar al’amura a kasar Kongo, wadannan su ne muhimman batutuwan da suka shiga kannun rahotannin jaridun Jamus akan al’amuran Afurka a wannan makon.

Da farko Somaliya. Barazanar da dakarun Musulmi masu zazzafan ra’ayi suka yi na shiga yakin sunkuru a Mogadishu ta tabbata gaskiya, inda tuni mataimakin P/M Hussein Aidid ya bayyana fargabar shiga wani hali irin shigen na Iraki. Jaridar Frankfurter Rundschau tayi bitar rikicin tana mai cewar:

“Tun da farkon fari kwararrun masana al’amuran Somaliya ke gargadi a game da yiwuwar sake komawa gidan jiya a kasar Somaliya inda ba doka da oda sakamakon fafatawar da Amurka da kawarta Habasha suka shiga yi da dakarun kotunan musulmi da sunan yaki da ta’addanci, inda suka ce shiga zauren shawarwarin shi ne kawai zai taimaka a shawo kann matsalar a cikin ruwan sanyi. A yanzun ana fama da bata kashi da zub da jini tsakanin sojojin Habasha da dakarun kotunan musulmi dake yakin sunkuru, sannan su kuma al’umar kasar Somaliya suka sake samun kansu a cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi.“

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung bayyana mamakinta na yi a game da yadda ake muzanta wa ‚yan gudun hijirar Somaliya tare da tuhumarsu da kasancewa ‚yan ta’adda a kasar Kenya. Kuma ba kowa ce ke da alhakin wannan mummunan mataki na keta hakkin dan-Adam ba illa kasar Amurka. Jaridar ta ambaci hukumar ‚yan gudun hijira ta MDD tana mai bayanin cewar:

„’Yan gudun hijirar suna cikin mawuyacin hali, ba su da muhallin zama, ba su da abinci kuma ba su da ruwan sha. Sannan ita hukumar kanta bata da ikon taimaka musu. Dukkan wadannan lamarin ya saba da yarjeniyoyi na kasa da kasa dangane da kyautata makomar ‚yan gudun hijira. Ita kuwa kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Human Rights Watch tara bayanai tayi a game da ‚yan gudun hijirar da aka cafke aka kuma tesa keyarsu zuwa Kenya inda suke fuskantar tambayoyi daga jami’an leken asirin Amurka, a yayinda ita Habasha kuma ta kame wasu ‚yan Somaliyar, wadanda a bisa ta bakinta wai ‚yan ta’adda ne.“

Wakilai na dindindin a kwamitin sulhu na MDD na ci gaba da matsin lamba domin ganin an dauki tsauararan matakai akan kasar Sudan domin ta canza salon kamun ludayinta dangane da yankin Darfur. To sai dai kuma ba a lardin Darfur ne kadai ake fama da tabrbarewar al’amura ba, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta nunar, inda take cewar:

„Bisa ta bakin mataimakin sakatare-janar na MDD akan taimakon jinkai John Holmes ya ba sanarwar cewa matsaloli a kasashen Chadi da janhuriyar Afurka ta Tsakiya daidai suke da halin da ake ciki a lardin Darfur, kuma har yau dakarun sa kai na kasar Sudan suna ci gaba da kai hare-hare a harabar Chadi, inda a wajejen karshen watan maris da ya gabata suka kashe mutane kimanin 400 a Chadin.“

A cikin wata sabuwa kuma a wannan makon wasu ‚yan gudun hijirar Afurka dake fafutukar shiga kasar Spain sun kai farmaki kann jami’an tsaron gabar tekun kasar tare da kokarin cunna wa jirginsu na sintiri wuta. A lokacin da take ba da wannan rahoton jaridar Der Tagesspiegel cewa tayi:

„Wannan dai shi ne karo na farko da aka fuskanci irin wannan tabargaza kuma ga alamu ‚yan gudun hijirar sun yi hakan ne saboda gudun ka da a sake mayar da su gida. To sai dai kuma hakan bata fisshe su ba, domin isarsu tsuburin Gran Canaria ke da wuya aka danka su hannun ‚yan sanda kuma za a tura su zuwa kasar Mauritaniya domin fuskantar shari’a.”