1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

April 25, 2007

Zaben Nijeriya shi ne ya fi daukar hankalin masharhantan jaridun Jamus a wannan makon

https://p.dw.com/p/Btvf
Zabe a Nijeriya
Zabe a NijeriyaHoto: AP

Ko da yake jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al’amuran dake faruwa a sassa daban-daban na nahiyar Afurka, amma fa zaben Nijeriya shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun a wannan makon, misali jaridar Die Tageszeitung, a cikin rahoton da ta bayar tayi tsokaci ne da alkawarin da shugaba mai barin gado Olusegun Obasanjo yayi lokacin da ya kama ragamar mulkin kasar Nijeriya, inda yayi alkawarin aiwatar da tsattsauran garambawul daga tushensa, amma fa sai ga shi zai bar wani babban tabo a baya..Jaridar ta kara da cewar:

“Akasarin al’umar Nijeriya sun gaji da gafara sa basa ganin ko kaho. A dai lokacin da shugaba Obasanjo ya dare kan kujerar mulki sai da yayi wa jama’a alkawarin cewar shi kansa zai sa ido wajen ganin cewar al’umar kasa baki daya sun samu isasshen makamashi, amma fa a yanzun jim kadan kafin barinsa gado duka-duka abin da mutane kan samu daga hukumar lantarki ta Nepa bai wuce wutar lantarki ta tsawon awa hudu a rana ba a duk fadin Nijeriya. Bugu da kari kuma al’umar kasar na zargin shugabansu mai barin gado da sauran masu nfada a ji a Nijeriyar da shirya wata makarkashiya ta magudi a mataklan da aka dauka na mayar da kamfanonin gwamnati ga hannun ‘yan kasuwa masu zaman kansu.”

Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

“Tuni murna ta koma ciki dangane da fatan da al’umar Nijeriya suka yi game da kyautatuwar makomar rayuwarsu karkashin mulkin shugaba mai barin gado Olusegun Obasanjo. Domin kuwa a bayxa ga gazawar da yayi wajen cika alkawurrukansa na yakar cin hanci da rashawa daga bisanin na Obasanjo ya dauki matakai iri-iri na danniya a kokarin murkushe abokan adawarsa, misali sai da ya tura wa mataimakinsa Atiku Abubakar jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC domin hana shi shiga takarar zaben Nijeriyar.”

Ga alamu dai jami’an diplomasiyyar MDD ba su sikankance da alkawarin da gwamantin Sudan tayi ba a game da kara karfafa rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afurka a Darfur. Dalin wannan dari-dari kuwa kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta nunar shi ne kasancewar fadar mulki ta Khartoum ta sha yin irin wannan alkawari ba tare da ta cika ba. A sakamakon haka kasashe kamarsu Amurka da Birtaniya suke dagewa akan lalle sai an kakaba wa Sudan takunkumin karya tattalin arzikinta.”