1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

June 22, 2007

Har yau ana neman cimma tudun dafawa a rikicin Cote d'Ivoire

https://p.dw.com/p/BtvG

Hali da ake ciki a Cote d’Ivoire da kuma hukunci na farko da aka zartar a shari’ar masu miyagun laifukan yakin Saliyo na daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon. Amma da farko zamu fara da wani rahoto da aka samu a wannan makon a game da yunkurin juyin mulkin da aka yi ikirarin wanzuwarsa domin kifar da mulkin shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe, A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

“Rahoton da wata jarida mai zaman kanta a klasar Zimbabwe ta bayar a game da gurfanar da wasu hafsoshin sojan kasar gaban kotu da aka yi domin amsa laifin wani yunkuri na juyin mulki, wanda aka ce wai sun yi kimanin shekara daya suna shiryawa, ko da yake gwamnati bata fito fili ta tabbatar da wannan zargi ba, inda take cewar magana ce da ta shafi rashin da’a tsakanin sojojin Zimbabwe, amma a hakika hakan na mai yin nuni ne da cewar ita kanta gwamnatin shugaba Robert Mugabe ta ankara da gaskiyar cewa a yanzu al’amuran shugaban.”

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a ganinta rahoton yunkurin juyin mulkin kage ne kawai a kokarin kawar da hankalin jama’a daga mawuyacin hali na tattalin arziki da Zimbabwe ke ciki. Jaridar ta kara da cewar:

“A halin yanzu haka Zimbabwe na fama da karayar darajar takardun kudinta da ta haddasa hauhawar farashin kaya da misalin kashi dubu uku da dari bakwai cikin dari, wadda za a iya cewar Zimbabwen ma ta fi kowa bajinta a wannan bangaren a duk fadin duniya. Akasarin gonakin da aka kkwace daga hannun manoma farar fata suna nan ne kwance ba a aiwatar dasu saboda irin shuka da taki da sauran kayan aiki.”

A can kasar Cote d’Ivoire, ko da yake an kafa gwamnatin hadin gambiza tsakanin shugaban kasa Laurent Gbagbo da ‘yan tawaye, amma babu wani ci gaban da ake samu akan hanyar zaman lafiya mai dorewa a kasar, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta lura ta kuma kara da cewar:

“Ko da yake dukkan sassan biyu na ikirarin sha’awar zaman lafiya a kasar Cote d’Ivoire, amma babu wani ci gaban da ake samu a duk lokacin da ake batu game da wasu kwararan matakan da zasu taimaka a cimma tudun dafawa sai ka ga ba a samun wani ci gaba. Babbar maganar dake hana ruwa gudu kuwa ita ce ta kwance damarar makaman dakarun sa kai dake ba wa shugaba Gbagbo goyan baya, wanda shi ne matakin farko kafin a kai ga kwance damarar makaman dakarun ‘yan tawayen, sai kuma maganar mahkunta da ta dan kasanci, wadda asalan ma dai ita ce ummalaba’isin rikicin kasar ta Cote d’Ivoire.”

A wannan makon kotun musamman ta MDD ta yanke hukunci akan wasu mutane uku a shari’ar da take yi akan masu miyagun laifuka na ta’asar yakin Saliyo, mai makobtaka da Cote d’Ivoire. Wannan rahoton ma jaridar Die Tageszeitung ce ta gabatar da shi inda take cewar:

„Shekaru biyar bayan kama aikinta a wannan makon kotun musanmma ta MDD akan miyagun laifukan yakin Saliyo ta yanke hukunci akan wasu tsaffin jami’an gwamnatin sojan kasar, wadanda tare da taimakon kungiyar tawaye ta RUF da gwamnatin shugaba Chalres Taylor a Liberia suka tafiyar da mulki. Ana samesu da laifukan ta’asa akan farar fula da kashe-kashe na gilla da fyade da bautar da mata da yara kanana.“

Sabon shugaban kasar Faransa Sarkozy ya kira taron kasa da kasa domin neman bakin zaren warware rikicin Darfur a Sudan, amma a cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung da kyar ne kwalliya zata mayar da kudin sabulu game da wannan taro domin kuwa hatta su kansu kawayen Faransar na Kungiyar Tarayyar Turai suna tababa game da tasirin taron da za a gabatar a ranar 25 ga wata..