Afurka a jaridu | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 15.02.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a jaridu

Sharhin Jaridun Jamus akan Afurka

default

Minista Frank-Walter Steinmeier a Togo


Ghana/Togo/Burkina Faso/Zimbabwe


Ghana

A wannan makon ne ministan harkoki n wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya kai ziyara a wasu kasashe uku na yammacin Afurka, wadanda suka hada da Ghana da Togo da kuma Burkina Faso. Wannan ziyarar dai tana daya daga cikin batutuwan da suka ɗauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus, inda jaridar Süddeutsche Zeitung ke cewar:


"Tun bayan da kasar China ta fara yada angizonta a kasashen Afurka a fafutukar cin gajiyar albarkatun kasa da Allah Ya fuwace wa nahiyar, kasashen Turai a nasu bangaren suka shiga gwagwarmayar kare makomar bukatunsu a Afurka, wannan kuma na daya daga cikin dalilin da suka sanya shuagabanni da manyan jami'an siyasa na Turai ke yawaita kai ziyara Afurka yanzu haka.

Kenya

An dai samu kyakkyawan ci gaba a yunkurin da tsofon sakatare-janar na Majalisar Ɗunkin Duniya Kofi Annan ke yi domin sasanta rikicin kasar Kenya, amma fa duk da haka har yau da sauran rina a kaba kafin a kai ga lafar da kurrar rikicin da ya biyo bayan zaben kasar a watan disamba mai zuwa, a cewar jaridar kimiyya da siyasa ta Stiftung Wissenschaft und Politik, a cikin wani dogon bayanin da tayi akan wannan rikici ta kuma bayyana ra'ayin cewar:

"Hanya mafi a'ala wajen dinke barakar siyasa da tashe-tashen hankulan da ake fama da shi a kasar Kenya shi ne matakai na diplomasiyya, amma ba neman kakaba takunkumi ko tsuke bakin aljifun taimakon raya kasa ga kasar ta gabacin Afurka ba. Ba shakka nuna wa gwamnatin Kenyar bacin rai da barazana yana da muhimmanci, amma duk wani mataki na takunkumin da za a dauka zai yi mummunan tasiri ba ma akan kasar kadai ba har da sauran kasashe makobta da suka dogara kacokam akanta domin tafiyar da hulɗoɗinsu na cinikayya da ketare."

Zimbabwe

A watan maris mai zuwa ne aka shirya gudanar da zaben shugaban kasa da majalisar dokoki a kasar Zimbabwe a yayinda a daya bangaren kasar ke fama da rikici na siyasa da tattalin arziki, inda aka kiyasce yawan marasa aikin yi ya kai kashi 80% na illahirin al'umar kasar. Jaridar Frankfurter Rundschau ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Duk wani yunkuri na dinke barakar siyasar Zimbabwe bai cimma nasara ba a yayinda take kuma ci gaba da fama da mawuyacin hali na tattalin arziki da hauhawar farashin kaya. Takardar kudi mafi girma a Zimbabwe ita ce ta dalar Zimbabwe dubu 750, wadda duka-duka abin da mutum zai iya saya da ita bai wuce sandan burudi guda ba. Al'amuran kiwon lafiya sun tabarbare a yayinda aka kiyasce yawan masu kwayar cutar Aids zai kai kashi 40 zuwa 50% na al'umar Zimbabwe. Ita kuma gwamnati tana nan tana kaka-nika-yi da marayun da suka yi asarar iyayensu sakamakon wannan cuta mai karya garkuwar jiki.

Uganda/Tchadi/Sudan

Afurka dai nahiya ce dake fama da rikici iri dabam-dabam, kama daga yake-yake na basasa da gwagwarmayar kama madafun iko da bala'o'i daga Indallahi. A takaice matsaloli sun kai wa wannan nahiya iya wuya a cewar jaridar Der Tagesspiegel, wadda ta lissafta jerin kasashen da rikicinsu ya ki ci ya ki cinyewa. Jaridar ta fara da kasar Kenya tana mai cewar:

"Kimanin mutane dubu daya suka yi asarar rayukansu sannan wasu sama da dubu 300 ke kan hijira sakamakon rikicin da ya biyo bayan zaben watan disamban da ya gabata a kasar Kenya. Tun bayan barkewar wannan rikici mutane sama da dubu 30 suka yi asarar guraben aikinsu a bangaren yawon shakatawa da Kenya ke tinkaho da shi wajen samun kuɗaɗen musaya na ketare. A makobciyarta Somaliya, tun abin da ya kama daga 1991 ake fama da rikici kuma kasar bata da wata tsayayyar gwamnati ta tsakiya. Idan an koma Sudan kuma za a ga cewar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma bayan yakin basasa na tsawon shekara 20 a kudancin kasar bai kawo wamni canji na a zo a gani ba. Shi kansa rikicin na Sudan yana da nasaba da mawuyacin halin da ake ciki a kasar Chadi mai karbar bakoncin dubban 'yan kudun hijirar Darfur a yammacin Sudan. Ita kuwa Uganda fama take yi da 'yan tawayen LRA a arewacinta.