Afropress | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.08.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afropress

Sharhin Jaridun Jamus kan nahiyarmu ta Afirka musamman halin da ake ciki a Mauritaniya.

default

Halin da aka shiga a Mauritaniya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi


To a wannan makon dai batutuwan da suka fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus dangane da al'amuran nahiyarmu ta Afurka sun hada ne da juyin mulkin soja a Mauritaniya da kuma rahoton da kasar Ruwanda ta gabatar inda take kalubalantar kasar Faransa cewar tana da hannu dumu-dumu a makarkashiyar kisan kiyashin da ya wakana a kasar a shekara ta 1994. A lokacin da take sharhi akan wannan zargi jaridar Berliner Zeitung cewa tayi:


"Tilas a shiga tababa a game da zargin da zai fito daga wata kasa dake karkashin mulkin kama karya akan wata kasa ta Turai dake bin tafarki na demokradiyya akan cewar tana da hannu a wani mataki na kisan kare-dangi. Amma fa akwai cikakkun bayanai dake tabbatar da hakan. A hakika kasar Faransa ta taimaka wa kawayenta 'yan Hutu tsakanin watan yuni da agustan shekara ta 1994 duk kuwa da cewar duniya gaba daya ana sane da ta'asar kisan kiyashin dake wakana akan 'yan Tutsi a daidai wannan lokaci. Kasar Faransa daidai da ita kanta MDD ba ta tabuka kome wajen dakatar da ta'asar ba, abu mafi muni ma shi ne tare da izinin MDD Faransar ta killace yankunan tsaro, inda masu alhakin ta'asar suka samu mafaka."


Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a cikin nata sharhin nuni tayi da cewar:


"A fafutukarta ta tabbatar da angizonta a tsakiyar nahiyar Afurka kasar Faransa tayi watsi da makarkashiyar ta'asar kisan kiyashin dake wakana a Ruwanda akan 'yan Tutsi, wadanda dakarunsu na tawaye ke samun goyan baya daga kasar Uganda mai amfani da harshen Turanci. A halin yanzu kuma a maimakon ta hakikance da kurakuranta fadar mulki a birnin Paris sai kokari take yi ta sa kafa tayi fatali da sakamakon binciken da aka gudanar akan rawar da ta taka a wannan ta'asa."


A kasar Mauritaniya ta yammacin Afurka sojoji sun yi juyin mulki ba tare da zub da jini ba. Bisa ga dukkan alamu kuwa musabbabin wannan mataki shi ne canje-canjen da shugaba Sidi Ould Cheikh Abdallahi ya aiwatar ne tsakanin manyan hafsoshin sojan kasar. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ci gaba tayi da cewar:


"Shi dai hambararren shugaba Sidi Ould Cheikh Abdallahi shi ne na farko da aka nada ta hanyar zabe na demokradiyya a kasar Mauritaniya tun bayan samun 'yancin kan kasar daga Faransa a shekara ta 1960. To sai dai kuma a baya ga matsaloli na cikin gida da aka yi zaton an shawo kansu bayan zaben na shekarar bara, akwai matsalar hare-haren da Mauritaniya ke fama dasu daga wasu kungiyoyi masu zazzafar akidar addini wadanda ke fafutukar shigar da abin da suka kira wai juyin juya hali daga Aljeriya zuwa Mauritaniya."


Masu sauraro karshen sharhin jaridun na Jamus akan al'amuran Afurka ke nan. Rabi gare-ki.