1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika ta Tsakiya ta bukaci taimakon MDD

Ramatu Garba Baba MNA
September 22, 2017

Shugaban Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta taimaka wa kasarsa da karin dakarun wanzar da zaman lafiya tare da dage takunkumin da ta aza mata kan sayen makamai.

https://p.dw.com/p/2kYTD
Faustin Archange Touadera
Hoto: imago/Pacific Press Agency

Shugaba Touadera ya mika kokon baransa ga Majalisar a yayin da yake gabatar da jawabinsa a taron Majalisar da ke gudana a birnin New York na kasar Amurka. Shugaban ya ce Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na cikin wani hali inda take fuskantar barazanar tsaro daga kungiyoyi na masu tayar da kayar baya, kafin ya kuma yi kira ga majalisar na taimaka mata da kayayyakin agaji ga miliyoyin mutane da yaki ya daidaita.

Mutane fiye da dubu dari shida ne suka rasa matsuguni a rikicin da ya biyo bayan tunbuke tsohon shugaba Francois Bozize baya ga wasu sama da dubu dari biyar da suke gudun hijra yanzu haka a wasu kasashe da ke makwabtaka da kasar.