Afrika na fuskantar barazanar yunwa a bana | Labarai | DW | 12.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afrika na fuskantar barazanar yunwa a bana

Wani rahoton hukumar abinci ta MDD yace nahiyar Afrika na kara fuskantar barazanar karancin abinci cikin wannan shekarar.

Darektan hukumar na yankin kudancin Afrika Amir Abdalla yace akwai alamun cewa canjin yanayi musamman a kudancin Afrika yana barazna ga albarkatun abinci na bana.

Yace kasashe da dama na yankin sunyi fama da mabaliyar ruwa da kuma fari wadanda dole a sake duba halinda suke ciki yanzu.

Kasashen da abin ya shafa sun hada da Angola,Madagascar,Mozambique Namibia da Zambia.