1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika A Jaridun Jamus

Lawal, TijaniMay 30, 2008

Sharhunan jaridun Jamus akan Afrika

https://p.dw.com/p/E9nH
Shugaban Sudan Omar al-Bashir, dana Chad President Idriss Deby,Hoto: AP


South Afrika/Tchad/Sudan/Nigeria


Hatta a wannan makon ma halin da ake ciki a Afirka ta Kudu shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus duk da cewar tun abin da ya kama daga ranar litinin da ta wuce al'amura sun fara sararawa. Kamar yadda jaridar DIE Tageszeitung ta nunar inda take cewa:


"Bayan makonni biyu na tashe-tashen hankula a yankunan bakar fata na Afirka ta Kudu, wanda ya salwantar da rayukan mutane sama da hamsin da tserewar sama da mutum dubu 30 daga ta'asar makobtansu bakar fata, an samu sararawar al'amura tun daga ranar litinin da ta wuce. To sai dai kuma suka da kakkausan harshe da shugaba Thabo Mbeki yayi a game da wannan mummunar ta'asa, wadda ta zubar da mutuncin kasar Afirka ta Kudun, ba ma a idanun al'umar Afirka kadai ba, har ma da sauran sassa na duniya, ya zama tamkar ihu ne bayan hari, saboda jawabin nasa ya zo a makare. Bugu da kari kuma a yayinda shugaban ANC Jacob Zuma da sauran jami'an siyasar Afirka ta Kudun suka ziyarci wuraren da wannan danyyen aiki da hali na rashin sanin ya kamata ya afku, shi shugaba Mbeki bai leka wurin ba, lamarin da ya sanya jaridar Sunday Times ta Afirka ta Kudun take cewar wajibi ne yayi murabus".

South Afrika

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta zargi gwamnatin Afirka ta Kudu ne da gazawa. Jaridar ta ce:

"Wadannan hare-hare na kyamar baki ba kome ba ne illa wani bangare na tabargaza iri dabam-dabam da gwamnatin Afirka ta Kudu take fama da ita." Jaridar ta kara da cewar:

"Gwamnati da illahirin jami'an siyasar Afirka ta Kudu sun gaza. Mutum daya da ya kamata a yaba mawa ita ce Winnie Mandela, wadda bata yi wata-wata ba wajen kai dauki ga mutanen da ta'asar kashe-kashen gillar ta rutsa da su a yankunan bakar fatar".

Tchad/Sudan

Ita kuwa majallar Der Spiegel tana tattare ne da ra'ayin cewar wannan tabargazar an dade ana shirya ta kuma jami'an siyasa da dama na da hannu dumu-dumu a cikinta a saboda haka duk mai sha'awar gasar ci kofin kwallon kafa ta duniya tilas ya sake tunani.

Duk da cewar kungiyar tarayyar Turai ta tsugunar da sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Chadi to sai dai kuma akwai masu korafin cewar babu wani dalili na tsugunar da sojojin a kasar. Amma a baya-bayan nan an samu jita-jitar cewa wai kasar Sudan na kulle-kullen shirya juyin mulki a kasar, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:

"Bayanai sun ce wai shugaba Al-Bashir na Sudan, shi ne ya nema daga shugaba Omar Bongo na kasar Gabon da ya shawo kan shugaba Sarkozy na Faransa da ya dauki wani matsayi na dan ba ruwansa a shirin kasar Sudan na kifar da gwamnatin Chadi. An kuma gabatar da jerin sunayen wadanda zasu kama madafun iko a kasar bayan wannan juyin mulki, abin da ya hada har da Mahmat Nour, wani tsofon jami'in diplomasiyyar Chadin, wanda ke da goyan bayan kasar Saudiyya. Kuma wai shugaba Ghaddafi na Libiya na da masaniya akan wannan batu. A hukumance dai sojojin kiyaye zaman lafiyar na kungiyar tarayyar Turai suna da wani matsayi ne na ba ruwansu, amma idan har Sudan zata tura mayaka zuwa N'Djamena to kuwa ba za'a kwashe lafiya ba."

Nigeria

A cikin wata sabuwa kuma sakamakon wani binciken da aka gudanar ya nuna cewar hatta sojan kiyaye zaman lafiya na MDD da kuma ma'aikata da dama na kungiyoyin taimako masu zaman kansu suna da hannu dumu-dumu a matakai na muzantawa da yi wa 'yan mata fyade a sansanoninsu na neman mafaka da taimako. Jaridar Die Welt ce ta ba da wannan rahoto.


A wani binciken kuma da ake ci gaba da yi ana zargin kamfanin gine-ginen nan na Bilfinger da tabargazar ba da toshiyar baki a fafutukar neman karin kwangila a Nijeriya. Mujallar Der Spiegel dake rawaito wannan rahoto ta ce reshen kamfanin na Bilfinger a Nijeriya Julius Berger na da hannu a tabargazar gabatar da toshiyar baki na miliyoyin dalar Amurka ga jam'iyyar PDP dake mulki a Nijeriya domin neman kwangilar gina wani bututun gas a kasar. Wannan shirin dai an dade ana gudanar da bincike kansa dangane da kamfanonin dake fafutukar neman kwangilar daga kasashen Faransa da Amurka.