1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika a jaridun Jamus

Lawal, TijaniApril 29, 2008

Sudan/Ruwanda/Ghana

https://p.dw.com/p/DqnO
Sudan/DarfurHoto: AP

A wannan makon halin da ake ciki a ƙasar Sudan shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus ta la'akari da samun shekaru biyar ga yaƙin lardin Darfur, amma har yau ba a samu bakin zaren warware rikicin ba. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar Süddeutsche Zeitung mai matsakaicin ra'ayin siyasa cewa tayi:

“Sabbin matsalolin da suka kunno kai a sassa daban-daban na duniya ya sanya aka yi watsi da makomar ƙasar Sudan. A yanzu babban abin da ke ci wa mutane tuwo ƙwarya shi ne matsalar tsadar rayuwa a kasashen Afurka da na Asuiya da kuma na Karibiya. Sai kuma rikicin lardin Tibet na ƙasar China da kisan kiyashin da ya wakana a ƙasar Kenya da kuma fafutukar dan kama karyar ƙasar zimbabwe Robert Mugabe wajen murƙushe sakamakon zaɓen ƙasar da aka gudanar watan da ya gabata. Amma fa sai tare da ɗaukar matakan diplomasiyya na ƙasa da ƙasa ne za a kai ga warware rikicin Sudan.”

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung mai ra'ayin mazan jiya, a cikin nata sharhin cewa tayi:

“Yau shekaru biyar ke nan cir da fara kashe-kashe a lardin Darfur, amma fa har yanzun kafofi na ƙasa da ƙasa sun kasa cimma nasarar dakatar da tashe-tashen hankulan. A yayinda ake ci gaba da samun karuwar dubban daruruwan ‘yan gudun hijira daga lardin, kungiyar taimakon abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsayar da shawarar ƙayyade yawan kayan bukatun yau da kullum da take jigilarsu zuwa yankin sakamakon farmakin da ake kai wa ayarin motocinta dake ɗauke da kayan taimakon. Al'amuran tsaro sai daɗa taɓarɓarewa suke saboda har yau ba a cimma kashi 40% na yawan sojojin kiyaye zaman lafiya da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Ƙungiyar Tarayyar Afurka suka yi niyyar Turawa yankin ba.”

A cikin wani abin da ake gani tamkar mummunar taɓargaza ce daga ɓangaren gwamnatin Jamus dangane da zaman lafiyar Ruwanda, a wannan makon jaridar Die Tageszeitung ta rubuta sharhi tana mai cewar:

“Abin kunya ne ganin yadda mahukuntan Jamus suka zura wa ƙungiyar FDLR mai iƙirarin fafutukar tabbatar da mulkin demoƙraɗiyya a Ruwanda take shirya matakanta na ta da zaune tsaye a harabar ƙasar, saboda hakan ya yi daura da abin da gwamnatin a fadar mulki ta Berlin ke yayatawa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samar da bunƙasa a nahiyar Afurka. Lokaci yayi da Jamus zata fito fili ta bayyana matsayinta dangane da rikice-rikice a yankunan dake ƙuryar tsakiyar Afurka.”

A wannan makon ƙasar Ghana ta karɓi baƙoncin Ƙungiyar UNCTAD ta Majalisar Ɗinkin Duniya mai sa ido a al'amuran ciniki da raya ƙasa. Amma fa a ɗaya ɓangaren ƙasar kanta na fama da taɓargazar ciniki da ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai dake fitar da kajinsu masu araha zuwa Ghana tare da kashe kasuwar cikin gida ta ƙasar. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar Financial Times Deutschland cewa tayi:

“Alƙaluma sun bayyana cewar kimanin tan dubu tara na gaɓoɓi da kayan ciki na kaji ake fitarwa daga ƙasashen Turai zuwa Ghana a duk shekara. Harkar na tafiya ba ƙaƙƙautawa saboda makiwata na ƙasar Holland na da ikon cinikin kajin akan farashi mai rafusar gaske sakamakon tallafin da suke samu daga gwamnati. Hakan na mummunan tasiri akan harkar kiwo ta cikin gida, inda a yanzu haka yawan abin da makiwatan na Ghana ke sayarwa bai wuce kashi 11% ba, a maimakon kashi 95% a farkon shekarun 1990.”