Afrika A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 06.05.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afrika A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a kasar Togo da kasashen dake makobtaka da ita shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus

Cibiyar al'adun Jamus da ake cunna mata wuta a Lome

Cibiyar al'adun Jamus da ake cunna mata wuta a Lome

Hatta a wannan makon mai karewa, jaridu da mujallun Jamus sun fi mayar da hankali ne akan halin da ake ciki a kasar Togo, dangane da tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben kasar, wanda kuma ake fargabar yaduwarsa zuwa kasashen dake makobtaka da ita. A lokacin da take sharhi game da haka jaridar DER TAGESSPIEGEL cewa tayi:

“Tashe-tashen hankulan dake faruwa a kasar Togo ka iya tad a zaune tsaye a yammacin Afurka, kuma kasashen Ghana da Benin dake makobtaka da ita kai tsaye sune suka fi fuskantar barazana. Domin kuwa tun bayan billar tashe-tashen hankulan dubban ‘yan gudun hijira ke kwarara zuwa wadannan makobtan kasashe. Kimanin ‘yan gudun hijira dubu 16 da 500 hukumar ‘yan gudun hijira ta MDD UNHCR a takaice tab a wa kariya a kasashen Ghana da Benin. Wadannan tashe-tashen hankula, wadanda suka kai ga kone cibiyar al’adun Jamus ta Goethe dake Lome, fadar mulkin kasar, sun biyo bayan zaben da aka gudanar ne kusan makonni biyun da suka wuce, inda aka ce Faure Gnassingbe, dan marigayi Eyadema, shi ne ya cimma nasara.”

Ita kuwa jaridar Handelsblatt, bias ga ra’ayinta, ita kanta sabuwar gwamnatin Togo ce ke neman fakewa da guzuma domin ta harbi karsana, inda take dora wa Jamus laifin tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben da aka gudanar ba a bisa ka’ida ba a kasar ta yammacin Afurka. Jaridar sai ta kara da cewa:

“Ba zato ba tsammani rikicin kasar Togo ya rutsa da Jamus, wacce ta mulki kasar daga shekarar 1884 zuwa ta 1914, inda aka kai hari kan cibiyar al’adunta ta Goethe dake birnin Lome. Wannan kuwa shi ne karo na farko da aka kai irin wannan hari kan wata cibiyar al’adun Jamus a ketare. Kuma akwai abubuwa da dama dake shaidar cewa mahukuntan kasar ta Togo na da hannu dumu-dumu a wannan mataki. Tuni ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yayi kira ga sakatare-janar na MDD Kofi Annan day a sa baki domin kawo karshen wannan rikici.”

Ita ma jaridar DIE ZEIT dake fita mako-mako ta leka kasar Togo inda tayi sharhi tana mai cewar:

“Kasashen yammacin Afurka, daya bayan daya suke fadawa cikin mawuyacin hali na rikici da tabarbarewar al’amuran tsaro. A halin yanzu haka kasashe kamar Saliyo da Liberiya tuni suka zama kango sakamakon yake-yakensu na basasa. Kasar Guinea na fuskantar barazanar tarwatsewa, a yayinda makekiyar kasa ta Nijeriya ke kaka-nika-yi da rikice-rikicenta na kabilanci da addini. Ita kuwa kasar Cote d’Ivoire, wadda ada can take da ci gaban tattalin arziki, sannan a hankali al’amuranta ke tabarbarewa sakamakon yakin basasa. Ita kuwa mitsitsiyar kasar Togo, duk da kankantarta, amma fa rikicinta ka iya daukar wani mummunan fasali, muddin gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afurka bat a samu ikon dakatar da shi ba. Tsaffin kasashen da suka yi wa Togo mulkin mallaka, kamar Jamus da Faransa ka iya bad a tasu gudummawar bias manufa.”

A wani sabon ci gaba kuma, dukkan sassan da basa ga maciji da juna a kasar Mali sun dukufa wajen neman hadin kan kasarsu domin dorata akan wata nagartacciyar hanya ta ci gaban kasa, a cewar jaridar GENERAL-ANZEIGER, wadda ta kara da cewar:

“Dukkan kabilun kasar Mali kama daga Tuareg da Songhoi da Bellah zuwa Fulbe da Bozos da ragowarsu, wadanda a zamanin baya suke gaba da juna, a yanzu suna bakin kokarinsu wajen neman hadin kai domin kyautata makomar ayyukan noma a kiwon dabbobi a tsakaninsu. Wannan shiri na noman rani da aka tanadar tare da taimakon hukumar taimakon fasaha ta Jamus GTZ yana da nufin yaki ne da matsaloli na talauci, wadanda ke daya daga cikin abubuwan dake taimakawa wajen billar rikice-rikice a kasashen Afurka.”