Afrika a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 23.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afrika a Jaridun Jamus

Kasashen Sudan da Zimbabwe da Afrika ta kudu da kuma batun kwllon klafa sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

Berti Vogts, sabon mai koyar da yan wasan Super Eagles na Nijeriya

Berti Vogts, sabon mai koyar da yan wasan Super Eagles na Nijeriya

To daga cikin al’amuran da suka fi daukar hankalin jaridun Jamus game da nahiyar Afrika a wannan mako, har da yadda matsalar kasar Sudan ta zama gagara-badau, sai halin da ake ciki a kasar Zimbabwe da matsayin Afrika ta kudu a majalisar dinkin duniya, inda a wnanan wata take shugabancin kwamitin sulhu, sai kuma batun kwllon kafa inda jaridu suka yi sharhi game da makomar wasannin cin kofin duniya a Afrika ta kudu a shekara ta 2010 da kuma aikin dake gaban sabon mai koyar da yan wasan Super Eagles na Nijeriya, wato Berti Vogts.

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara sharhin ta ne da cewar a karshe dai an fara samun wani shugaba na Afrika da ya daga muryar sukan manufofin mulkin kama karya na Robert Mugabe a Zimbabwe. Shuigaban Zambia, Levy Mwanawasa ya kwatata mulkin Mugabe a matsayin jirgin ruwa ne dake neman nitsewa, yayin da ma’aikatan sa suke kokarin ceto shi kot a halin yaya. Jaridar tace siyasar nan ta zurawa shugaban na Zimbabwe idanu da kasashen kudancin Afrika na kungiyar SADC suke yi, tareda fatan zai canza manufofin sa don kashin kansa yaci tura. Lokaci yayi da wadannan kasashe zasu fito fili su nunawa Mugabe din iyakar sa. Danagane da haka ne shugaba Mwanawasa na Zambia yace kungiyar SADC zata yi zaman taron gagawa a Daresalam ranar Litininm ai zuwa domin duba halin da kasar ta Zimnbabwe take ciki.

Ita kuwa jaridar General Anzeiger ta kwatanta halin Zimbabwe din ne a matsayin mumunan abu ga nahiyar Afrika. Tace mummunan matakin da gwmanatin kasar take dauka kann yan adawa, idan ba’a yi hankali ba, yana iya zama yain basasa, abin da zai shafi makomar Zimbabwe gaba daya.

Jaridun Frankfurter Allgemeine Zeitung da Tagestzeitung duka sun yi sharhunan su ne kann kasar Sudan. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi tsokaci da sabani a majalisar dinkin duniya a game da yadda za’a bullowa rikicin dake addabar kasar ta Sudan. Tace akwai alamun hukumar kare hakkin yan Adam ta majaisar ba zata sami nasarar jan hankalin wakilan ta, suyi Allah wadai da matakan keta hakkin jama’a a yankin Darfur ba, saboda kasashen China da Rasha suka hana duk wata tattaunawa kann al’amarin. Jaridar Tageszeitung a daya hannun tace ganin yadda aka kasa samun wani ci gaba a kokarin warware rikicin na Darfur, ina za’a nufa kann kasar ta Sudan. Jaridar ta ambaci tsohon wakilin musmman na majalisar dinkin duniya kann Sudan, Gerhard Baum, wanda yace Sudan ta zama wata alama ta rashin tabuka wani abin kirki daga majalisar dinkin duniya. Duk da kudirri da taruka da hukumomi na neman zaman lafiya da ake dasu, amma rikicin Sudan ba gagara. Jaridar Tageszeitung tace daya daga cikin kasashen dake da alhakin ganin kashe kashe suna ci gaba a Darfur ita ce China, saboda hana daukar duk wani mataki na takunkumi kann Sudan, bisa tsoron yin haka zai shafi bukatun ta a wnanan kasa.

To wai shin Afrika ta kudu zata sami nasarar shirya wasannin kwlalon kafa na cin kofin duniya a shekara ta 2010 kamar yadda aka shirya? Wannan tambaya ce ta dauki hankalin jaridar Tagesspiegel a wnanan mako. Jaridar ta ambaci mashawarcin hukumar kwllon kafa ta duniya, wato Fifa, Horst Schmidt, wanda ya amsa tambayar da cewar babu shakka wasanin zasu gudana a Afrika ta kudu a shekara ta 2010, kamar yadda aka tsara su. A nan Jamus dai ana ci gaba da samun rahotanni marasa dadin ji game da Afrika ta kudun. Bayan rashin ci gaba a kokarin shirya wasannin, Afrika ta kudun tana kuma fama da matsaloli na aikata manyan laiffuka da bata lokaci a aiyukan gine-gine da suka shafi wasnanin.

Daya daga cikin kasashen dake fatan shiga wasnanin na cin kofin duniya a shekara ta 2010, ita ce Nijeriya. A farkon wnanan wata kasar ta kafa tushen farko a kokarin cimma wnanan buri nata, lokacin da tsohon mai koyar da yan wasan Jamus, wato Bert Vogts ya karbi aikin sa na koyar da yan wasan Super Eagles, kann hanyar su ta shiga wasannin cin kofin Afrika da kofin duniya. Jaridar Bild am Sonntag tace Vogts ba bako bane a game da wasannin cin kofin duniya ko na yankuna. A shekara ta 1996 ya jagoranci Jamus zuwa ga daukar kofin Turai, to amma yanzu Vogts din ya karbi aikin da zai zama mai matukar wahala a gareshi. Jaridar Bild am Sonntag tace Nijeriya dai ba baya take ba wajen rudami, musmman a fannin kwallon kafa. Tace abubuwa biyu da Vogts ya maida hankalin maimaita su a duk wadanda ya gana dasu bayan ya isa Nijeriya, sune ladabi da kyakkyawan tsari. Yace burin sa shine ya sake tsarin kwallon kafa a Nijeriya ya kuma shigar da ladabi ga yan wasa.