Afrika a Jaridu | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 02.01.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afrika a Jaridu

Sharhunan Jaridun Jamus kan Lamuran Afrika

default

Ghana/Mauritius/Somalia

Daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan al'amuran Afurka a wannan makon har da zaben kasar Ghana, inda jaridar Die Tageszeitung tayi sharhi tana mai cewar:

"Ba kome ya taimaka 'yan hamayya suka lashe zaben kasar Ghana ba illa girman kai na da nuna isa na masu rike da akalar mulkin kasar a yanzu. A sakamakon haka al'umar Ghana su kimanin miliyan 12 dake da ikon kada kuri'a suka koya musu darasi. Jam'iyyar dake mulki ta NPP ta kwashi kashinta a hannu ne tun a zagayen farko na zaben a ranar bakwai ga watan desamban da ya wuce, inda jam'iyyar hamayya ta lashe kujeru 114 ita kuma NPP ta tashi da kujeru 107 a majalisar dokokin kasar. Wannan nasarar da 'yan hamayya suka samu na mai yin nuni ne karara da rashin gamsuwar al'umar Ghana ta salon kamun ludayin gwamnatin NPP mai barin gado."

Ta la'akari da irin wannan kyakkyawan ci gaba da aka samu, jaridar GIGA Focus Afrika tayi amfani da wannan dama domin bitar rawar da sojoji suka sha takawa a siyasar kasashen Afurka tun bayan da kasashen nahiyar suka fara samun mulkin kansu zuwa yanzu. Jaridar ta ce:

Darfur UNAMID

"A dai halin da ake ciki yanzun juye-juyen mulki irin wanda ya faru a Mauritaniya a cikin watan afrilun da ya wuce ko kuma boren sojojin kamar wanda aka fuskanta a Guinea-Bissau watan nuwamban da ya gabata, ba kasafai ba ne ba, ake ganinsu a kasashen Afurka dake kudu da hamadar Sahara. Domin kuwa tun bayan kadawar iskar canji a shekara ta 1990 aka fara samun koma bayan juye-juyen mulkin soja, ko da yake har yau sojojin na ci gaba da taka rawa a manufofin cikin gida na wannan nahiya, inda ake da kasashe 19, wadanda a yanzu haka shuagabanninsu suke da toshen soji. Galibinsu kuwa sun dare kan karagar mulki ne sakamakon juyin mulki ko boren soji, amma daga baya suka kwabe kaki suka shiga takarar zabe domin ganin an nada su kan mulki a demokradiyyance."

A wannan makon shugaban kasar Somaliya Abdullahi Yusuf ya kakkabe hannuwansa daga al'amuran mulkin kasar. A lokacin da take sharhi game da haka jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

Abdullahi Yusuf Präsident von Somalia

"Murabus din shugaban Somaliya Abdullahi Yusuf, a hakika shi ne mafi alheri ga makomar wannan kasa. Domin kuwa ba wani abin da ya tabuka illa hana ruwa gudu ga kokarin sasanta rikicin kasar a tsawon shekaru hudu da yayi yana jan akalar shugabancinta. A yanzun bayan murabus dinsa, wata sabuwar dama zata bude domin shiga sabbin shawarwarin sulhu da magance rikicin kasar da yakin basasa yayi kaca-kaca da ita. Wani abin kuma da zai taimaka a kokarin sasanta rikicin Somaliya shi ne canza salon tunanin gaggan kasashe irinsu Amurka da Turai da China da kuma Indiya, wadanda dukkansu suka lashi ba da gudummawa wajen murkushe fashe-fashen jiragen ruwa na jaura da ake fama da shi a tekun baharmaliya. Amma fa ba a nan ne gizo ke saka ba, ainifin matsalar Somaliya, tushenta na cikin gida ne, a saboda haka ya kamata a nemi bakin zaren warwareta a siyasance. Domin kuwa maztsawar da ba a shawo kan rikicin ba, to ba shakka za a ci gaba da fama da fashe-fashen jiragen ruwan".