1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Yamma za ta yaki hijira zuwa Turai

Uwais Abubakar Idris
August 3, 2017

Shugabanin hukumomin kula da shige da ficen jama’a na kasashen Afrika ta Yamma sun yanke shawarar amfani da fasahar zamani domin dakile matsaloli bakin haure da ke tururuwa zuwa kasashen ketare musamman kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/2hexJ
Westafrikas Staatschefs bei ECOWAS Summit
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Mummunan hali na azabtarwa da yunwa da ma mace-mace da bakin kan shiga a kokarinsu na barin kasashensu don zuwa nahiyar turai bisa hasashen samun aljannar duniya na zama babban kalubalen da ke fuskantar kasashen kungiyar ta ECOWAS, domin akwai mutanen yankin da dama da suka shiga wannan hali, kuma babu alamun samun sauki saboda matsaloli mabanbanta. Abin da ya fi daga hankalin kungiyar ta ECOWAS din shi ne yadda manufarta ta sakarwa al’umma mara su kai da komowa a yankin ke fuskantar barazana ta rashin tsaro saboda yadda bakin ke kai kawo. Wannan ya sanya sake lale ta hanyar amfani da fasahar zamani domin dakile masu mumunan hali.

Libyen Küstenwache rettet Flüchtlinge auf dem Mittelmeer
Bakin haure masu kokarin shiga TuraiHoto: Getty Images/AFP/T. Jawashi

Ibro Faruq wakili daga jamhuriyar Nijar, kasar da mafi yawan bakin ke bi su suna shigewa kasashen na Turai, kasar da a yanzu ke fuskantar martsaloli na tsaro, sakamakon kwarrar bakin, ya bayyana muhimmancin musayar bayanai a tsakanin kasashen kungiyar ta ta kasashen Afirka ta Yamma, wanda a shawararsa zai iya ingtanta yanayin tsaro. A yayinda kasashen wannan kungiya suka yanke shawarar amfani da katin zamani don dakile masu aikata  laifuffuka ta fakewa da walwalar kai da komowa, ana cike da fatan ganin tasirinsa a aikace a yankin da ake fama da matsaloli na  ta’adanci da safarar jama’a da da ake kai su kasashen turai.