Afirka ta nemi adalci kan batun yanayi
Masana kimiyya sun yi gargdin cewar zafin duniya zai karu da misalin hudu a ma'aunin Celcius ya zuwa karshen wannan karni. Afirka tuni ta fara shan wahala daga canjin yanayin.
Afirka tana fuskantar karancin ruwa
Bankin duniya ya yi kiyasin cewar idan zafin duniya ya karu da misalin biyu a ma'aunin Celcius, yankin kudancin Afirka zai yi fama da karancin misalin kashi 30 cikin 100 na yawan ruwan sama. Sakamakon hakan shi ne karuwar barazanar fari. A lokacin da aka yi fama da karancin ruwan sama a tsakiyar shekaru na 90, Habasha ta yi asarar akalla rabin dukkanin dabbobinta.
Ruwan sama fiye da kima
A yankin gabashin Afirka ana iya samun ruwan sama fiye da kima nan gaba - a wasu 'yan kwanaki kalilan cikin shekara. A 2011 ruwan sama mai karfin gaske ya shafi birnin Dar es Salaam mai tashar jiragen ruwa a Tanzaniya, abin da ya haddasa ambaliya a dukkanin birnin inda tilas aka kwashe mutane 10.000 da nema masu matsuguni na gaggawa, kuma akalla mutane 23 suka mutu.
Karuwar matsalar yunwa saboda karancin albarkar noma
A Afirka kananan manoma ne ke samar da kashi 90 cikin 100 na albarkatun noma a nahiyar. Idan har ba a kyautata noman kayan amfanin gona da ke iya jure wa fari da ambaliyar ruwa da sauran bala'o'in da suka shafi yanayi ba, za a sami karin kashi 20 cikin 100 na 'yan Afirka da za su yi fama da yunwa ya zuwa shekara ta 2050, bisa kiyasin Majalisar Dinkin Duniya.
Hadari ga lafiyar jama'a
Karancin abinci mai gina jiki sakamakon rashin kaka mai albarka tuni ya fara zama matsala a kasashe da dama. Mutane da yawa sukan yi kaura zuwa manyan birane inda cututtuka kamar kwalera suke yaduwa cikin gaggawa. Idan aka sami karuwar zafi, wasu cututtuka kamar Malariya suna iya yaduwa cikin hanzari - misali a yankin nan mai tsaunuka na Afirka ta Gabas, yankin da yanzu ba shi da cutar Malariya.
Bacewar jinsin halittu
Karuwar zafi ya kan shafi rayuwar jinsin halittu. Jinsin tsire-tsire da dabbobi masu yawa ba sa iya daidaita kansu da canjin yanayi da ake samu cikin gaggawa. Wani rahoto na hukumar kula da yanayi ta kasa da kasa ya ce tsakanin kashi 20 zuwa kashi 30 cikin 100na dukkanin jinsunan halittu ne suke fama da barazanar bacewa sakamakon canjin yanayi.
Babu sauran kankara a tsaunin Kilimanjaro
An yi misalin shekaru dubu 12 ana samun kankara kan tsaunin Kilimanjaro. To amma daga shekaru 100 da suka wuce zuwa yanzu, kankara a tsaunin ta ragu da kashi 80 cikin 100. Wata tawaga ta masu bincike daga Ohio ta yi kiyasin cewar idan hakan ya ci gaba, kankara a tsaunin za ta bace gaba daya ya zuwa shekara ta 2033. Suka ce karancin ruwan sama da karancin zubar dusar kankara su ne dalilan hakan.
Idan aka sare bishiya ta karshe......
Mafi yawan alhakin haddasa samun canjin yanayi yana tattare ne da tashoshin makamashi, masana'antu da ababen hawa a Amirka da Turai da Asiya. To amma sare dazuzzuka a kasashen Afirka da dama, misali domin samar da gawayi, abu ne da ke haddasa karuwar iskar Carbon Dioxide a sararin samaniya, abin da ke taimakawa ga lalata kasar noma.
Dashen bishiyoyi don farfado da dazuzzuka
Mutane da yawa yanzu sun gano cewar tilas ne su dauki matakan da za su dakatar da canjin yanayi. 'Yan Kenya masu da'awar kare muhalli sun yi shekaru gwammai suna dashen sabbin bishiyoyi, tare da samun fadadar yankunan da suka zama dazuzzuka yanzu. Bishiyoyin sukan hana zaizayewar kasar noma mai albarka, sukan kuma shanye iskar CO2 mai haifar da canjin yanayin sararin samaniya.
Kariya ta hanyar noma amfanin gona iri iri
Noma amfanin gona iri daya yana iya sanyawa a fada hadarin fari ko annobar kwari. Idan aka shuka kayan amfanin gona iri iri ana iya samun amfanin gona mai yawa ko da wasu daga cikinsu sun gamu da wani bala'i. A bisa rahoton hukumar kare muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) noma amfanin gona iri iri a wuri guda yana iya kara karfin kariya daga barazanar canjin yanayi fiye da noma na al'ada.
Daukar matakai na zahiri amma ba jawabai kawai ba
Amfani da rijiyoyin ruwa na karkashin kasa da tsarin inshora ga manoma idan kaka ta ki albarka - wadannan na daga cikin hanyoyi masu yawa na sassauta matsalolin canjin yanayi. Taimakon raya kasa da matakan kare yanayi tilas su tafi kafada da kafada, kamar yadda wakilai suka nunar a taron Majalisar Dinkin Duniya a baya-bayan nan. Sai dai har yanzu ba a gabatar da shirin wasu aiyuka da za a yi ba.
An dora fata kan taron birnin Paris
"Adalci a fannin yanayi yanzu!"- kamar yadda 'yan zanga-zanga suka yi ta kira lokacin taron yanayi a Afirka Ta Kudu shekaru hudu da suka wuce. 'Yan zanga-zangar yanzu sun maida idanunsu a karshen wannan shekara lokacin da za a tattauna batun canjin yanayi a Paris. A taron, ana iya amincewa da tsari na farko na duiya baki daya game da canjin yanayi, bisa manufar takaita illar canjin yanayin.