Shugaba Zuma zai kalubalanci hukuncin babbar kotu
May 24, 2016Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana shirin kalubalantar kotun kasar da ta nemi a sake nazarin shari'ar da ake zarginsa da laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa da suka tasamma 800 kamar yadda ofishin shugaban ya bayyana.
A wani jawabin da ofishin shugaban ya fitar a yammacin ranar Litinin ya ce matakin da kotun ta dauka wani abu ne da ya shafi mutuncin shugaban kai tsaye, kuma kotun na yin kuskure a wasu ayyukanta.
A watan da ya gabata ne dai babar kotun kasar ta Afirka ta Kudu ta bayyana bukatar sake nazarin tuhume-tuhume da ake wa shugaban wadanda aka ajiye su a shekarar 2009, matakin da babbar kotun ta ce an yi shi ne bisa kuskure.
Masu gabatar da kara a kasar dai ta Afirka ta Kudu sun bayyana cewa za su kalubalanci hukuncin kotun da ke tuhumar shugaba Jacob Zuma da wadannan laifuka, matakin da ya samu suka a kasar, abin da ake ganin kokari ne na ba wa shugaban wata dama ta hana doka ta yi aiki a kansa.