1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Afirka ta Kudu tayi kira ga ƙasashe masu hannu da shuni su taimakawa yankin Darfur.

Ƙasar Afirka ta Kudu, ta yi kira ga ƙasashe masu hannu da shuni, da ƙungiyoyin bada agaji na ƙasa da ƙasa, su himmantu, wajen kai tallafi domin samo bakin zaren warware rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Afirka ta Kudu ta buƙaci ƙasashen su bada kayan aiki ga rundunar ƙasa da ƙasa da Majalisar Ɗinkin Dunia zata aika a Darfur.

A nata ɓangare ,Afirka ta Kudu, ta alƙawarta yin nazari, ga buƙatar da Majalisar Ɗinkin Dunia ta gabatar, don samun tallafin jiragen sama masu durra angulu a yankin Darfur.